BUDADDIYAR WASIKA: A DAKATAR DA ABIN KUNYA NA “RANAR MAKA” A CIKIN MAKARANTUN MU NA SAKANDARE
Daga Mai kishin Ƙasa
Read also: Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Ziyarartar Makarantun Kwana
Zuwa ga Iyaye da shugabannin makarantu da malamai da ɗalibai da Ma’aikatar Ilimi. Na rubuta wannan buɗaɗɗiyar wasiƙa cikin tsananin damuwa da rashin jin ɗadi kan yadda bukin murnar kammala jarabawar ‘yan sakandare ta ƙarshe da ake wa laƙabi da taron ranar”Marker Day” ke ƙara ta’azzara da kuma yaɗuwa a makarantun sakandaren ƙasarmu, musamman a lokacin jarrabawar ƙarshe ta NECO da WAEC.
Wannan ba bikin nasarar ilimi ba ne. Yana nuna rashin ɗa’a da rashin tarbiyya da rashin mutunta duk wani abu da ilimi da al’adunmu suka horas ne.
Menene Ranar “MARKER DAY”?
Wanna wata rana ce ta ƙarshen jarabawar kammala makarantar sakandare da ɗalibai ke gudanar da bikin da kuma nuna rashin ɗa’a a fili ƙarara ga malaman su da abokan karatunsu da ma al’ummar gari baki ɗaya.
A wannan rana ce ɗalibai ke yaga tufafin su ko rubucce duk rigar makarantarsu da kalaman da suka ga dama, duk kuwa da kyan kalmomin ko akasin haka da zuba foda ko fenti a kan riguna juna (uniform ), game da waƙe-waƙe da raye-raye a kan titi ba tare da kunya ko tsoron ababban hawa ka iya buge su ba.
Yunwa: Sakamakon Rashin Abinci Mai Gina Jiki Yara Sama da 650 Sun Halaka a Katsina -MSF
Daliban kan zagaya harabar makarantar su cikin hayaniya da hargitsi da kuma wani lokacin tashin hankali, kai kace hari aka kawo makarantar ko kuma duk inda suka dosa a unguwanni.
A lokacin irin wannan ɗalibai ke kece raini tare da bayyana kalaman batanci ga malaman da suka basu ilimi, walau na addini ko na zamani gami da cin mutuncin mahukuntan makarantar da yin watsi da duk dokokin da aka sanya a makaranta da faɗace-faɗace, wai da suna yanzu sun sami ‘yanci.

Mafi muni kuma shi ne, wasu ɗaliban kan ci zarafin abokan karatunsu musamman mata waɗanda suka zaɓi ba za su shiga wannan mummunar ta’ada ba. Suna riƙe su da ƙarfi, suna zuba musu abubuwa a sittirunsu, suna rubutu a kan (uniform)da jikinsu ba tare da son ransu ba. Yawancin waɗannan ‘yan mata suna kuka, suna kokawa, kuma suna ƙoƙarin su yi fito na fito da su, amma sun fi ƙarfin su saboda sun fi su yawa kuma ‘yan matan na jin kunya a cikin jama’a.
Wannan ba biki bane. Wannan cin zarafi ne, cin mutumci ne da wulaƙanci gami da rashin ɗa’a.
Read also: Gwamnatin Kano ta Sanar da Ranar konawa Makaranta
Me yasa Muke So A Kawo Karshen Wannan Bikin na “Markers Day”?
Wannan rana ko biki na ɗalibai bashi da wani muhimmanci ko tarihi a cikin tsarin ilimi ko al’adar bahaushe, haka kuma waɗannan halayyar ɗalilai da na shimfiɗa a ƙasa na daga cikin manyan hujjoji da muke ganin ya kamata wanna rashin ɗa’a ya kawo ƙarshe ta hanyar haɗa ƙarfi da karfe musamman tsakanin masu ruwa da tsaki a fanin ilimi:
1. Yana Rusa Al’adunmu da ma shafe su daga doron ƙasa baki ɗaya: Kamar yadda aka sani al’adunmu suna da tasiri ta inganta mutuntaka da koyar da ladabi da kunya. Ranar “Marker Day” tana yaƙi da duk waɗannan ɗabi’u na gari dana lissafa, wai da suna “biki.”
2. Ya Saɓa da Koyarwar Addininmu: Ko kai musulmi ne ko mai bin addinin kiristanci, babu wani addini da ya ƙarfafa sanya suturar da ba ta dace ba, da cin zarafin jama’a, ko ƙwacen waya ko sata ko lalata kayan makaranta ko na jama’a da suna wani nau’i na farin ciki ko bikin.
3. Yana cutar da ‘ya’yanmu: A maimakon koyar da alkhairi, ana koyawa yara rashin bin doka da ɗa’a. Wannan ya shafi dukka masu laifi da marasa laifi, wato waɗanda ke binsu domin kallo, musamman ‘yan matan da ake zalunta da wulaƙanci. Haka zalika yin wanna ta’ada na ƙara nuna ƙyama ga waɗanda basa son karatun boko ko kuma jefa tunani cikin zukatan su, anya malaman na nusar da yaran alkhairi kuwa?
Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
Roƙona da Kira a Aikace ga waɗannan muhimman bangarori kamar haka:
-IYAYE: Ya zama wajibi iyaye su tashi tsaye domin sanin abin da ‘ya’yen su ke aikatawa musamman idan sun zo jarabawar ƙarshe ta kammala makarantar gaba da furamare. Kada ku ba da kuɗi domin sayen riguna na Ranar “Marker” ko ba da kuɗi don ƙarfafa wannan taron abin kunya da suna wai tayya murna ko biki.
Ya kamata ku koya wa yaranku bikin samun nasarori akan komai ta hanyoyin na mutunci da godiya gami da tsoron Allah tare da addu’ar neman samun nasara a jarabawar da suka rubuta.
-SHUGABANIN MAKARANTA DA MASU MULKI:
A hana bikin “Marker Day” a jihohi da ma ƙasa baki ɗaya. Domin bikin ba shi da gurbi a kowace babbar cibiyar ilimi, walau a jiha ko a tarayyar ƙasa.
Haka kuma a kare lafiya da haƙƙin kowane ɗalibi, musamman waɗanda suka ƙi shiga bikin duk da ƙoƙarin takwarorinsu na turssasa ta kai musu hari da tsangeama da makamantansu.
Ya zama wajibi a tabbatar an kama tare da ladabtar da duk ɗalibin da aka samu yana wanna bikin, kuma shugabanni su dawo da martabar makarantu kamar yadda aka san su a shekarun da suka gabata.
– MALAMAI:
Da akwai buƙatar malamai su ke nusar da ɗalibai rashin amfanin bikin da kuma asarar da ke ciki gami da bayyana hukuncin da ka biyo baya ga ɗalibin da aka kama.
A ilmantar da dalibai cewa ana nuna murnar nasara ta hanyar mai kyau da godewa Allah Maɗaukakin Sarki, ba ta hanyar tsatsaga riga ko shafa fenti ko halin rashin ɗa’a da sace-sace ba.
-MA’AIKATAR ILIMI:
Ya cancanta a jinjina wa jihar Yobe da jihar Kano bisa jagoranci gwamnonin su da suka sanya dokar hana yin bukukuwan tunawa da ranar ‘Marker’ a dukkan makarantun dake jihohin. Saka idanu da kuma hukunta duk wata makaranta da ta ba da damar gudanar da irin wannan taro da kuma ɗaliban da aka kama da karya doka domin hukunta su.
Amfanin ilimi shine domin a gina al’umma da kuma cusa ɗabi’a ga matasa, ba don ƙarfafa tashin hankali da cin mutuncin jama’a ba.
-DALIBAI:
Ina mai baku shawara da ku girmama kanku da koyi da gwarzayen shugabanni ta hanyar karatu tuƙuru domin zamantowa iyaye abin alfahari. Sakamakon jarrabawar ku yana da mahimmanci fiye da yin bikin, yana da mutukar muhimmanci bayan kammala jarabawar a bita da addu’a gami da roƙon Allah don samun nasara.

Ka da ku turssasa abokan karatunku ko tilasta wa kowa ya shiga Ranar ‘Marker’. Wannan zalunci ne, kuma abin kunya ne kuma Allah zai hukunci ga duk wanda ya aikata hakan.
Ka sanya uniform ɗinka cikin alfahari da girmamawa, shine zai tasiri wajen jagoranci samun cigaban ka, ba halin rashin mutunci da yaga tufafin ko bata su da maka ba.
Read also: Babu Bukatar Lissafi Don Shiga Tsarin Koyon Arts da Humanities – Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana
Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Ya kamata mu yi aiki tukuru yanzu. Mu kare martabar makarantunmu da makomar yaranmu. Dole ne kiyaye doka da oda, Kada mu yaɗa rikici tsakanin jama’a kuma mu kira shi da suna biki ko murnar nasara. Idan muna so ilimi ya inganta da sanya ɗabi’u na gari ga yara, gami da tanadin gobe, to dole ne a kawar da ranar ‘Marker’ tun daga yanzu har kuma abada.
Ma rubuci, Dan kishin ƙasa.




























