Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
Daga Sunusi K/Na’isa
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi, dangane da belin wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Dan Wawu.
Gwamnan ya bayar da wannan umarni ne bayan da aka samu zazzafar martani daga al’umma, sakamakon rahotannin da ke nuna cewa an ga sunan kwamishinan a cikin takardun gwamnati da suka shafi sakin wanda ake zargin.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar.
Gwamnatin Kano Ta Ce Za Ayi Adalci Ga Ɗaliban Da Aka Kashe, ‘Yan Sanda Sun Kama Ɗalibai 11
Don fuskantar wannan batu, Gwamna Yusuf ya kafa wani kwamitin bincike na kat ta kwana karkashin shugabancin Mashawarcinsa na Musamman kan Harkokin Shari’a da Sabunta Kundin Tsarin Mulki, Barista Aminu Hussain. An dora wa kwamitin nauyin binciko gaskiyar lamarin da bayar da shawarwari kan matakin da ya kamata a ɗauka nan take.
Mambobin kwamitin sun haɗa da:
1. Barr. Aminu Hussain – Shugaba
2. Barr. Hamza Haladu – Mamba
3. Barr. Hamza Nuhu Dantani – Mamba
4. Alhaji Abdullahi Mahmoud Umar – Mamba
5. Manjo Janar Sani Muhammad (Mai ritaya) – Mamba
6. Kwamared Kabiru Said Dakata – Mamba
7. Hajiya Bilkisu Maimota – Sakatare.
Read also: YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO
Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Yayin da yake bayyana kafa kwamitin, Gwamna Yusuf ya nuna matukar damuwarsa kan wannan zargi na rashin gaskiya, inda ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ci gaba da yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi da kuma yaki da duk wasu munanan ɗabi’u a cikin al’umma.




























