Kano na Alhini Rashin Mahaifiyar ‘Yan Biyar, Ta Rasu Bayan Haihuwa
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
Al’ummar Jihar Kano sun fada cikin jimami da alhini bayan rasuwar wata mata da ta haifi ‘ya’ya biyar a lokaci guda, inda ta bar jariran guda biyar.
Matar ta haifi jariran ne a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano a ranar Laraba, amma rahotanni sun ce ta rasu washegari.
Jami’in hulda da jama’a na Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano, Labilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya tabbatar da hakan a sakon da ya aikewa Global Tracker a ranar Alhamis.
Read also: Alamun Murar Tsuntsaye ta Bulla A Kano, Gwamnati ta Ce Babu Fargaba
Gobara Ta Kone Gidaje, Na’urar Wutar Lantarki a Kano
Lamarin ya jawo hankalin jama’a tun farko sakamakon yadda haihuwar ‘yan biyar ke da matukar wuya. Sai dai rasuwar uwar ta kara sanya tausayi da alhini a fadin jihar.
Kwararrun likitoci sun bayyana cewa irin wannan haihuwa ta ‘ya’ya da yawa na da matukar wuya kuma galibi tana tattare da manyan hadurran lafiya wanda ka iya kaiwa ga rasa rai. Haka kuma irin wannan ciki na sanya gagarumin nauyi ga jikin uwa tare da kara yiwuwar samun matsaloli kafin da bayan haihuwa, in ji masana kiwon lafiya.
Read also: Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
Kwamishina ‘Yan Sanda Ya Ce Sun Tattara Sunayen Masu Dillacin Ƙwaya A Kano Sama Da 2000
Ko da yake ba a bayyana ainihin musabbabin rasuwar matar ba, lamarin ya haifar da alhini mai yawa daga al’umma da masu fatan alheri, inda da dama suka bayyana wannan rashi a matsayin mai raɗaɗi, musamman ganin cewa jariran sun rage ba tare da kulawar mahaifiya ba.



























