Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano.
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Ƙarin Bayani Akan Tsarin Taimakekeniyar Lafiya ta Jihar Kano (KSCHMA)
Kwamishinan Lafiya na jiha, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana damuwarsa da yadda harkar kasuwancin magunguna ya tabarbare gami da shiga hali mara daɗi a jihar Kano a shekarun da suka gabata.
” Mun samu kasuwancin magunguna na jihar Kano, bayan ƙarewar shekaru takwas na zangon mulki na biyu na Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a cikin mummunan yanayi mara daɗi”. Dakta Labaran ya ce.
Kwamishinan, Dakta Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana hakan yayin da yake karɓar shugabannin Кungiyar Masu Haɗa Magunguna da Sarrafa su ta Najeriya, reshen jihar Kano, da suka ziyarci shi a ofishinsa.
Ya koka da cewa sun samu kasuwar magani, musamman Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Asibiti (DMCSA), hukuma ɗaya tilo da gwamnati ta amince ta samar wa asibitoci magunguna masu inganci da sauƙi, a sume tare da neman matsananciyar buƙatar kawo mata ɗauki a wannan lokaci.
Ka Iya Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Read also: Majalisar Dokokin Jihar Kano Zata Tallafawa Hukumar DMCSA Don Ta Cimma Gaci
Dakta Labaran ya yi farin ciki da samun dunƙulalliyar kasuwar hada-hadar magunguna a Ɗangwauro kasancewar abubuwa sun fara dawowa daidai, ya ƙara da cewa abin da kawai ya rage shi ne tilasta amfani da kasuwar yadda ya kamata domin a tsaftace kasuwancin magunguna a jihar.
Kwamishinan ya ce sirrin da ke tattare da samun nasarar ayyukan samar da magunguna a Kano ta biyo bayan neman shawarar ƙwararru kan harkokin magunguna da yake yi game da duk wani abu da ya shafi harkar kafin ya tura wa Gwamna jiha Abba Kabir Yusuf.
Ya bayyana cewa, gwamnatin Alhaji Abba Kabir Yusuf tana yin ayyukan da take yi ne domin al’umma, yana mai shawartar masu kasuwancin magani da su yi taka-tsantsan da jin tsoron Allah yayin da suke gudanar da ayyukansu, domin za a iya sake canja tare da sarrafa maganin da wa’adinsa ya ƙare a sake mayar da su kasuwa, yana mai yarda da cewa mutum mai tsoron Allah ba zai yi irin wannan ƙazamin kasuwancin ba.
Dakta Labaran ya ce ya yi farin ciki sosai da ɗaukar nauyin ɗalibai zuwa ƙasar Indiya su yi karatun haɗa magunguna da sarrafa su a lokacin da yake kwamishina a tsakanin shekarar 2011 da 2015, ya ce a lokacin ‘yan Kano masu rajista a wannan ilimin 51 ne kawai, wanda hakan ya sa Gwamna Kwankwaso ya umarce shi ya tantance mutum 100 aka tura su Indiya, da mafi yawansu yanzu haka suna hidimta wa jihar Kano.
Da yake jawabi tun da fari, Shugaban Кungiyar, Famasis Mustafa Umar ya ce sun zo ma’aikatar ne domin su nuna goyon bayansu ga ƙoƙarin kwamishinan na kawo sauyi a sashin lafiya na jihar nan.
Ya nuna farin cikinsa da cewa dawowar kwamishina ta zo a lokacin da ya dace saboda masu ilimin haɗa magunguna da sarrafa su na jihar Kano suna cikin damuwa mai tsanani game da makomar DMCSA, amma yanzu sun samu nutsuwa saboda abubuwa sun fara dawowa daidai, ta kai yanzu ake samun magani kashi 96 cikin 100 a asibitoci idan an kwatanta da baya da ake samun kaso 30 kawai.
Read also: Kano na Alhini Rashin Mahaifiyar ‘Yan Biyar, Ta Rasu Bayan Haihuwa
Shugaban ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa naɗa ɗaya daga cikinsu, Famasis Aminu Bashir a matsayin Babban Sakatare, wanda shi ne irinsa na farko a tarihin jihar Kano, yana mai tabbatar da cewa babban sakataren zai yi aiki tuƙuru wajen ci gaban aikin gwamnati duba da ƙwazo da jajircewarsa a aiki.
Ka Iya Karanta Wanna:Sojoji Sun Lakume Manyan Kwamandojin Bello Turji Guda 7, Da Sauran Yaransa 24
Jami’in Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim Abdullahi ya aiko mana cewa shugaban kungiyar ya sanar da kwamishinan cewa a watan Nuwamba, na wannan shekarar, jihar Kano za ta karɓi baƙuncin taron Кungiyar Masu Samar da Magunguna da Sarrafa su da ake sa ran ‘ya’yan ƙungiyar dubu uku zuwa dubu biyar za su ziyarci Kano, inda ya nemi gudummawar gwamnati.




























