Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi
Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki da jikin ɗan adam gaba ɗaya.
Read also: Likita Daya na Duba Marasa Lafiya 21000 A Jigawa
Dakta Sunusi Usman Na’ibi, ƙwararen likitan haƙori ne, ya yi mana bincike dangane da burushin wanke haƙora, wanda wasu kan ce ‘asuwakin Bature’.
Burushi haƙora wani abin wanke haƙora ne wanda aka samo asalinsa daga ‘suwak’ (kalma ce ta Larabci) da Bahaushe ke kiran sa da asuwaki.
Asuwaki yana da dogon tarihi, tun zamanin Annabi Muhammadu (SAW). A kan yi amfani da ɗanyen ko busasshen ice a matsayin asuwaki wajen goge haƙora domin kare lafiyar haƙoran da dadashi da hana warin baki da ma wasu cututtuan da ka iya addabar jikin mutum.
Burushin wanke haƙori, yana ɗauke da mariƙi da kuma kai, inda aka tanada don sanya sinadarin wanke haƙora domin tsaftace su da fitar da datti da abincin da ka iya maƙaɗewa bayan an gama ci, ko kuma wasu ƙananan cututtuka da ido ba zai iya gani ba wato (bacteria) da makamantan su.
MUHIMMANCIN YIN BURUSHI:
Ƴana daga cikin muhimmancin amfani burushi ya kare haƙora daga karyewa da kuma kamuwa da cututtukan dadashi da kuma hana bakin mutum wari da sauran su.
TASIRIN BURUSHI GA LAFIYAR BAKIN DAN’ADAM
Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi na iya tasiri wajen canza lafiyar baki ɗan’adam.
Ya kamata a canja burushi duk bayan wata uku, ko kuma idan an wanke bakin da ya kamu da ciwo (infection) ko kuma ya canja siffa wato burushin ya cinye ko kuma ya ɗanƙwashe.

Ɗanƙwasashe
WA YA KAMATA YA YI AMFANI DA BURUSHI?
Kowane rukuni na shekaru akwai irin burushin da ya kamata su yi amfani dashi kamar haka:
JARIRAI: Wannan rukuni, uwa ce ke da alhakin kula da lafiyar bakin jariri. Na sani wani ka iya tambaya me ya haɗa jariri da wanke baki? To! A nan likitocin haƙora sun ce yana da kyau a riƙa tsaftace dadashin jariri ta hanyar amfani da hankici mai tsafta bayyan an jiƙa shi da ruwa mai kyau, sannan a goge wa yaran dasashinsu bayyan shan nono ko abinci ga waɗanda suka kai fara cin abinci.

Burushi yara
Ƴan Shekara 1 zuwa 4: A waɗanan shekarun haƙora sun fara fitowa a baki. saboda haka ana buƙatar a fara wanke musu baki da burushi irin na yara mai laushi da man wanke baki mai sinadarin ‘flouride’.
Dole ne ya zama ana wanke musu baki, ba su za a bari su wanke da kansu ba saboda za su iya haɗiye man wanke bakin ko kuma su ƙi wanke bakin kamar yadda ya kamata.
Ƴan shekaru 5 zuwa 8: A wannan rukuni, yaro yana iya wanke baki da kansa amma ana buƙatar kulawa domin a tabbatar yana wanke bakin dai-dai. Sannan burushinsu zai zama mai laushi kuma burushin ya zamanto ƙarami yadda zai iya shiga bakin ba tare da wahala ba.
Shekaru 9 zuwa 60: Daga wannan shekara ana iya amfani da burushi mai matsakaicin karfi (medium) domin kare lafiyar haƙoransu.
Tsofaffi Sama da 60: Da yawan tsofaffi a kan same su da ciwon dadashi (sensitive) ko haƙora, saboda haka za su yi amfani da burushi mai laushi (soft).
Mutanen Da Ke Buƙatar Amfani da Burushi na Musamman:
1. Mashaya taba (sigari): Ana buƙatar su yi amfani da burushi mai ƙarfi (hard).
2.Masu Larurar shanyewar ɓarin jiki ko rashin ƙarfin jiki na buƙatar burushi da ke amfani da wutar lantarki (electric brush) ko kuma a samu wanda zai dinga yi mu su burushin.
Read also: Gwamnatin Tarayya Haɗin Gwiwa da Bauchi Sun Samar da Motocin Daukar Marasa Lafiya Kyauta

Burushin masu shanyewar ɓarin jiki
3.Ma su Haƙorin Roba (artificial teeth) za su yi amfani da burushi mai laushi (soft) wajen wanke haƙori, amma ba da man wankin haƙori ba.
LARURORI 7 DA KA IYA FARUWA SAKAMAKON RASHIN WANKE HAƘORA DA BURUSHI
Yayin da mafi yawan mutane ke sane da cewa rashin tsaftace baki na iya haifar da cututtukan da suka shafi dadashi da samar da rami a haƙora. Binciken masana ya nuna illar rashin wanke haƙora ta wuce iya baki kawai domin ya kan haifar da cututtuka kamar haka:
1. Ciwon Zuciya: An danganta rashin lafiyar baki da ƙaruwar haɗarin kamuwa da ciwon zuciya. Hakan yakan faru ne saboda ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar dadashi (gum) da ka iya shiga cikin jini su yi tafiya zuwa zuciya, suna haifar da kumburi kuma suna iya haifar da ciwon zuciya.
2. Cututtukan Numfashi: Rashin tsaftar haƙori na iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan numfashi kamar cutar huhu. Hakan na faruwa ne saboda ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar dadashi na iya shiga cikin huhu, wanda ke haifar da cututtuka da ka iya hana numfashi kamar yadda ya kamata.
3. Cutar Mantuwa: Bincike ya nuna cewa akwai alaƙa tsakanin rashin lafiyar baki da kuma ƙaruwar haɗarin kamuwa da cutar mantuwa. Ana tunanin hakan na faruwa ne saboda ƙwayoyin cutar da ke sa cutar dadashi ‘gum’ ta shiga cikin jini kuma ta yi tafiya zuwa ƙwaƙwalwa, wadanda ka iya haifar da kumburi da raguwar fahimta.
4. Ciwon Suga: Idan kana da ciwon sikari, yin watsi da lafiyar haƙori na iya haifar da sakamako mai tsanani. Yawan sikarin da ke cikin jini na iya sa cutar ‘gum’ ta yi muni, kuma cutar danko na iya sa ta yi wahala wajen sarrafa matakan sikari na jini.
5. Matsalar Juna Biyu:
An danganta rashin lafiyar baki mara kyau da ƙaruwar haɗarin matsalolin ciki kamar haihuwa, da kuma ƙarancin nauyin sinadaran haihuwar.
Hakan na faruwa ne saboda ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar dadashi na iya shiga cikin jini da kuma cutar da ɗan jaririn da za a haifa.
6. Rashin Ƙarfin Mazakuta: An danganta rashin lafiyar baki mara kyau da ƙaruwar haɗarin rashin ƙarfin mazakuta. Hakan na faruwa ne saboda ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar gum na iya lalata jijiyoyin jini, wanda ka iya haifar da matsalar rashin ƙarfin jini wanda shi ke kawo raunin mazakuta.
7. Ciwon Ƙoda: Daga ƙarshe, ƙin yin tsaftar haƙori kamar yadda ya kamata na iya ƙara haɗarin kamuwa da cutar ƙoda. Hakan na faruwa ne saboda ƙwayoyin cutar da ke haifar da cutar dadashi na iya shiga cikin jini kuma suna iya cutar da koda.
Don haka, ka tabbatar kana kula da tsabtar haƙoranka domin kare kanka daga cututtuka.
Kuma tsaftar haƙori ta hanyar yin burushi da man goge haƙora mai inganci na sa haƙora haske da walƙiya a kai a kai. Yin hakan zai sa haƙoranka da dadashi da ma dukkan jikinka su zauna lafiya.
ME ZA KA YI DOMIN INGANTA LAFIYAR BAKIN KA?
Waɗanan abubuwan da muka lissafa a ƙasa su ne muhimman abubuwan da ya kamata a lura da su domin inganta lafiyar baki kamar haka:
1. Burushi: Wanke baki da burushi a kullum safe da dare da man goge baki da likitocin haƙora suka yarda da su, na da mutuƙar muhimmanci ga lafiyar baki da haƙora.
Yin Burushi sau biyu na taimakawa wajen sakaci dattin da ke tsakanin haƙora ‘flossing’ akalla sau daya kullum yana da mutuƙar muhimmanci domin yana cire wasu ƙwayoyin cuta da fitar da abincin da ya maƙaɗe a tsakankanin haƙora, kuma ya kan tsaftace haƙora da sa su haske da sheƙi.
2. Ziyartar likitan hakora: Ana buƙatar duk bayan wata shida (6) a ziyarci likitan haƙora don tsaftace hakori ko kuma dubawa don kare haƙora daga kamuwa daga matsalolin hakori, waɗanda suka hadar da cututtukan dadashi da cinyewar haƙori da kuma warin baki da makamanta su.

Burush
3. A guji chafe-canfen al’adun gargajiya: Domin waɗanan na haifar da matsanantan ciwuka, kuma sukan sa kamuwa da cutar kansar baki da cututtuka masu wahalar da ɗan’adam.
4. Kaucewa kayan shaye-shaye: Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da giya da taba sigari na taimakawa ƙwarai da gaske wajen tabbatar da lafiyar baki.
Read also: Kwamishina Lafiya Ya Magantu, Yadda Suka Sami Kasuwancin Magunguna A Kano
5. Cin abinci mai gina jiki: Shin kun san cewa sirrin lafiyar hakora da dadashi na iya samuwa a cikin abincinku? Cin abinci mai gina jiki mai dauke da nau’in ajujuwan abinci, kamar nama da madara da ‘ya’yan itatuwa da kayan lambu da sauransu na iya taimakawa wajen kiyaye bakinka daga kamuwa daga nau’in cututtuka da kan addabi haƙora da baki da ma jiki gaba ɗaya.
Dr. Na’jbi, ƙwararai ne a fanin tiyatar haƙori, za a iya samunsa a numbar waya 0810697732, Email: Sunaibi46@gmail.com Fb; Na’ibi dental clinic Wahtapp:wa.me/+2348106977321 ko kuma ofishinsa a NA’IBI DENTAL CLINIC dake kan titin Gwarzo, daura da BUK first gate, jihar Kano, Nigeria.




























Pingback: UNICEF Ta Ce Yaro Ɗaya Na Mutuwa Daga Cikin 10 Sakamakon Rashin Tsaftattacen Makewayi - The StentorNews Hausa