NYSC: ADUSTECH Ta Karyata Rahoton Jinkirin Tura Dalibai, 1,763 Sun Samu Gurbi
Daga Wakilin mu
Jami’ar Aliko Dangote ta Kimiyya da Fasaha (ADUSTECH), Wudil, Jihar Kano, ta karyata rahotannin da ke cewa an samu jinkiri wajen tura wasu daga cikin ɗaliban da suka kammala karatu domin shiga shirin bautar ƙasa na NYSC.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Jami’ar ta bayyana wani rahoto da jaridar Alfijir News ta wallafa, wanda ya yi ikirarin cewa iyaye da wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa suna neman bayani kan jinkirin, a matsayin rahoto da aka gina bisa rashin samar da hadaddun bayanai kuma waɗanda ba su kammala ba.
A wata sanarwa da Shugaban Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗar da Jama’a na jami’ar, Abdullahi Datti Abdullahi, ya fitar, ADUSTECH ta ce babu wani dalibi da ya kammala karatu daga jami’ar a watan Satumban 2025, sabanin abin da rahoton ya nuna.
Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota
Ta bayyana cewa ɗaliban da ake magana a kansu sun kammala rubuta jarabawar shekarar ƙarshe ne kawai a watan Satumban 2025, inda ta jaddada cewa kammala jarabawa ba ya nufin cewa an kammala dukkan matakan karatu ba.
A cewar jami’ar, kafin a ayyana ɗalibi a matsayin wanda ya kammala karatu, akwai wasu matakai da suka haɗa da tantance takardun jarabawa da ba da maki da jarabawar waje, kammalawa da kare ayyukan shekarar karshe (Project), da kuma duba sakamakon a matakai daban-daban na jami’ar har zuwa amincewar Majalisar Dattawan Jami’ar.
Read also: An Gudanar Da Saukar Karatun Alqur’ani A Makarantar Ir’shadul Adfal Na Dalibai (58)
ADUSTECH ta ce sakamakon da Majalisar Dattawan Jami’ar ta amince da shi ne kawai za a iya miƙa shi domin ɗora sunayen ɗaliban a shafin NYSC.
Jami’ar ta kuma ce tana bin dukkan ƙa’idojin NYSC wajen gudanar da aikin (mobilization), ciki har da miƙa jerin sunayen ɗaliban da Majalisar Dattawa ta amince da su da kuma kwafin takardun zuwa hedikwatar NYSC.
A cewar jami’ar, ta samu nasarar tura ɗalibai 10,232 zuwa bautar ƙasa daga Batch A na 2024 zuwa Batch C na 2026. Ta ƙara da cewa ɗalibai 1,763 sun samu mobilization a Batch C na 2026, wanda aka fara rajistar sa ta yanar gizo a ranar 7 ga Satumba, 2026.
Jami’ar ta ce wasu daga cikin ɗaliban da ke hana wasu ɗalibai samun mobilization sun haɗa da rashin cike bayanan NYSC (biodata) da rashin miƙa fom ga Jami’in NYSC na jami’ar da rashin tabbatar da matsayin shigar ɗalibi ta shafin JAMB, da kuma rashin bin umarnin da aka bayar kan aikin mobilization.
ADUSTECH ta ce Sashen NYSC na jami’ar ya kafa tsarin tantancewa da tabbatar da bayanan ɗalibai kafin miƙa sunayensu ga NYSC, wanda ake gudanarwa tsawon shekaru uku domin rage kura-kurai a bayanan ɗalibai.
Jami’ar ta bukaci iyaye, masu kula da dalibai da dalibai da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa neman bayani daga hukumomin jami’ar da suka dace. Ta kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su riƙa tabbatar da sahihancin bayanai kafin wallafa rahotanni.
Read also: Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman
EFCC Ta Kori Ma’aikata Sama da 40, Ta Gurfanar da Biyar Kan Cin Hanci da Rashawa
Jami’ar ta sake jaddada kudirinta na kare muradun dalibai da inganta harkokin koyarwa da koyo, tare da gode wa iyaye, dalibai da sauran masu ruwa da tsaki bisa goyon baya da hadin kan da suke ba ta.




























