Daga Sunusi K/naisa
Makarantar Ir’shadul Adfal Al-Muhajirun Islamiyya da ke unguwar Lokon Makera, Kofar Na’isa a cikin garin Jihar Kano ta gudanar da saukar karatun Alqur’ani Mai Girma na dalibai 58; maza 18, mata 40.
Saukar karatun, wadda aka gudanar a filin Makera, ta samu armashi da halartar manyan mutane duk kuwa da ana cikin alhini na rashin daya daga cikin iyaye a wannan unguwa ta Lokon Makera, Malam Alkali Sammani.
A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Aliyu Ibrahim Abdulkadir wanda ya samu wakilcin Sarkin Yakin Gaya, Alhaji Sa’idu Madaki ya taya daliban murna da samun wannan nasara ta saukar Alqur’ani Mai Girma wanda ya bayyana Shi a matsayin tushen Ilimi na addini da kuma zamani.
Ya bukaci malamai da su fito da dabarar koyar da daliban da suka sami khatamar Alqur’ani domin koyar da su ilimin zamani, musamman na Turanci da lissafi domin samun wakilci nagari a duk inda suka sami kansu a rayuwa.
Kwamishinan Ma’aikatar Lafiya ta jiha, Dakta Abubakar Labaran Yusuf ya gode wa wadanda suka assasa makarantar tare da ba da tabbacin goyon bayan gwamnati karkashin jagoranci Alh. Abba Kabir Yusuf.
Dakta Abubakar ya kuma gode wa al’ummar yankin bisa karrama wasu zakakurai da suke ba da gudummawa a fannoni da dama ciki har da ma’aikatan sa kai na Asibitin Sarkin Dori Sulemanu.
Ya kuma bukaci kungiyar samar da ci gaba ta unguwar da su gabatar masa da duk abin da asibitin ke bukata cikin hanzari domin magancewa. Da Kuma bukatun makarantar a rubuce.
Read also: Makarantar Zam-Zam International ta Yaye Ɗalibai 28 Mahaddata Al-Qur’ani, Ciki Har da Asiya Usman
Haka Kuma Daktan ya ja hankalin iyaye da su rinka Kai ‘ya’yan su rigafi, musamman na cutar mashako da kyanda da za a fara a nan bada jimawa ba.
Tun da fari sai da Shugaban Makarantar Malam Ikiramatu Sa’id ya ce saukar karatun ita ce kashi na biyar bayan kafuwar makarantar tare da gode wa Malamai da iyayen yara bisa tallafi da goyon baya da suke ba su.
Malam Ikiramatu ya zayyano kadan daga cikin matsalolin da ke addabar makarantar musamman na rashin wadattatun dakunan karatu da (Aji) da isasun Malamai da abin zama da makamantansu.
Shugaban taro Alhaji Musbahu Rabi’u Danbaffa, ya kalubalanci daliban da su ci gaba da neman Ilimi, inda ya ce wannan mataki ne na farko a fagen Ilimi tare da sanya tsoron Allah a dukkan al’amuransu, daga bisani ya bada gudunmwar naira Dubu Ashirin ga makarantar.
Malam Jamilu Datti Wudilawa ya yi tambihi dangane da falalar neman ilimin Al’qurani tare da aiki da shi da kuma soyayya ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallam da son ahalinsa.
Sheikh Malam Ibrahim Inuwa Sagagi, Limamin Masallacin Juma’a na Ja’en shi ya gabatar da darasu ga daliban.
Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Kano Alh. Laminu Rabi’u Danbaffa ya bayar da gudummawar tabarmi ga makaranta.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Haka zalika, Sarkin Yakin Qadiriyya Dakta Shehu Abdulkadir ya ba da gudummawar Al’qurani guda 58 ga dalibai.
Yayin saukar, an gudanar da addu’o’i ga karamar hukuma da jiha da kuma kasa baki daya.




























