Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

An bukaci al’umar karamar hukumar Rano da su kara marawa kokarin gwamnatin jiha Kano na bunkasa harkokin ilmi.

Rano
Rano

An bukaci al’umar karamar hukumar Rano da su kara marawa kokarin gwamnatin jiha Kano na bunkasa harkokin ilmi.

Daga Yazid Sunusi Yahaya

Shugaban karamar hukumar, Malam Naziru Muhammad Ya’u Rano ya bayyana haka ya yin karama ma’aikatan da makarantun da ke karkashin sashin hukumar ilmin bai daya na shiyar Rano wanda aka yi a a da kin taron karamar hukumar a sakatariyar yankin na Rano.

Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano ya ce wasu daga cikin hanyoyin inganta harkar ilmin da gwamnatin jihar Kano bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta bujiro da su sun hada da warewa fannin ilmin kaso mafi tsoka a kasafin kudin bana da daukar malamai da samar da kayan koyo da koyarwa a makarantun jiha baki daya.

Wannan na cikin sanarwar manema labarai da da jami’in shiyar yada labarai na shiyar Rano Abdullahi Musa Gyadi Gyadi ya rabawa manema labarai a inda shugaban karamar hukumar ta Rano yara da cewa a bangaren majalisarsa za ta ci gaba da yin koyi da gwamnatin jihar ta hanyar baiwa fannin ilmin kulawa ta musamman don bukasa ilmi a tsakanin matasa maza da mata na yankin.

Kabilu Mazauna Malam Madori da Ƙaugama Sun Karrama Ɗan Majalisa Tarayya Hon. Makki Yalleman Bisa Kulawa Ga Ilimi

Daga nan sai bayyana cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen rabawa daliban karamar hukumar rigunan makaranta da littattafai da sauran kayan rubutu da karartu.

Ya yabawa wadanda aka karrama tare da jan hankalin su da sauran malamai da shugabannin makarantu da suyi amfani da karramawar wajen kara himma wajen aiwatar da ayyukan su.

Shugaban hukumar ilmin bai daya ta jihar Kano, Alhaji Yusuf Kabir Wanda ya samu wakilcin Dakartar ilmantarwa a hukumar, Alhaji Balarabe Danlami Jazuli ya nuna gamsuwarsa da yadda Mai martaba Sarkin Rano Dokta Muhammad Isah Umaru da shugaban karamar hukumar Malam Muhammad Naziru Ya’u Rano suke tallafawa fannin ilmin a yankin tare da kira da sauran Sarakuna da shugabannin kananan hukumominn jihar da su yi masarautar Rano a wannan bangaren.

Dangane da wadanda aka karrama kuwa, shugaban hukumar ilmin bai daya ta jihar Kano, yace kada su dauki karramawar a matsayin biyan su a kan kwazon da suke yi sai dai don su kara jajircewa a aikin su.

Ya ce bisa jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf hukumar ilmin bai daya ta jihar Kano za ta kara bullo da hanyoyin koyo da koyarwa da jin dadin malaman makarantun firamare.

Shugaban wakilin shugaban kungiyar Malamai ta jihar Kano da shugaban zauren sakatarorin ilmi na jiha kuma sakataren ilmi na karamar hukumar Garun Malam sun yaba da tsarin da ofishin shiyar ilmin bai daya na Rano ya bullo da shi na zakulo wadanda aka karrama din tare da kira ga na sauran shiyoyin da su yi da wannan tsarin.

EFCC ta Gurfanar Da Ɗan Austria Kan Boye Bayyana Wasu Maƙudan Kuɗaɗe $800,575 da €651,505

Tun da farko Daraktan shiyar ilmin ta Rano, a hukumar ilmin bai daya ta jihar Kano yace sun yi amfanii da hazaka da jajircewa da kamanta gaskiya da kyakkyawar gudunmawa wajen zakulo wadanda aka karrama.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...