An Caka wa Malamin Addini Wuka a Sakkwato, Masu Ibada Sun Kashe Wanda Ake Zargi
Daga Wakilin mu
Hankula sun tashi a wasu sassan birnin Sakkwato bayan da wani matashi ya caka wa wani malamin addinin Musulunci, Malam Musa Lukwa, wuka jim kadan bayan kammala Sallar Juma’a a masallacinsa da ke yankin Mabera.
An ce matashin, wanda ake kira Mai Barewa, yana cikin masu ibadar da suka halarci Sallar Juma’a, kuma yana zaune a daya daga cikin sahun gaba kafin ya kai wa malamin harin bayan an kammala sallar.
Majiyoyi sun ce wanda ake zargin ya caka wa Malam Lukwa wuka sau biyu a wuya, lamarin da ya jikkata malamin.
Daga bisani, masu ibadar sun yi nasarar cafke matashin, inda suka lakada masa duka har ya mutu.
Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya
An ce harin ya biyo bayan wata barazana da matashin ya yi a baya ta cewa zai kashe Malam Lukwa da babban dalibinsa, Malam Murtala Assada.
Bayan wannan barazana, malamin da mabiyansa sun kai rahoto ga ’yan sanda, wanda ya kai ga kama matashin tare da gurfanar da shi a gaban kotu.
Read also: An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano
Kotun ta bayar da umarnin a tsare shi a gidan gyaran hali yayin da shari’ar ke ci gaba. Sai dai kwanaki hudu kafin harin na ranar Juma’a, malaman sun ziyarci gidan gwamnatin jihar Sakkwato, inda suka gabatar da rubutacciyar korafi kan lamarin.
Da yake tabbatar da faruwar harin, kakakin rundunar ’yan sandan jihar Sakkwato, DSP Ahmad Rufa’i, ya ce Malam Lukwa na karbar magani a Asibitin Kwararru na Sakkwato.
Ya kuma tabbatar da cewa mabiyan malamin ne suka kashe wanda ake zargin bayan sun cafke shi.
Rufa’i ya ce kawo yanzu ba a kama wani mutum dangane da tashin hankalin da ya biyo bayan harin ba, yana mai cewa rundunar ta tura jami’ai tare da daukar matakan da suka dace domin hana lamarin kara ta’azzara.
Ya ce ’yan sanda na gudanar da bincike domin gano musabbabin harin da kuma tantance duk wadanda ka iya kasancewa da hannu a lamarin.
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Rundunar ta kuma yi kira ga mazauna birnin da su kwantar da hankula tare da guje wa duk wani mataki da zai iya kara dagula zaman lafiya, yayin da bincike ke ci gaba.




























