Connect with us

Hi, what are you looking for?

Tsaro

An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano

1768730266452
1768730266452

An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano

Daga Sunusi K/Naisa

Rundunar Ƴan sandan Jihar Kano ta sanar da cafke mutum uku da ake zargi da shirya tare da aiwatar da kisan gilla da aka yi wa wata matar aure da ƴaƴanta shida a unguwar Dorayi Chiranchi a ranar 17 ga Janairu, 2026.

Kakakin Ƴan sandan Jihar Kano CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa an samu nasarar cafke mutanen ne bisa umarnin Sufeto Janar na Ƴansanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, PhD, NPM, inda aka yi amfani da dabarun aikin tsaro na leƙen asiri.

Kiyawa, ya ce aikin kamen ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan Ƴan sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, tare da tawagar kwararrun jami’ai.

Gwamnan Kano Abba Yusuf Ya Umarci ‘Yan sanda su Gaggauta Kamo Waɗanda Sukai Kisan Gilla A Unguwar Dorayi

A sanarwar waɗanda aka cafke sun haɗa da Umar Auwalu, mai shekaru 23 daga Sabuwar Gandu ɗan uwa ga matar da Isyaku Yakubu, wanda aka fi sani da Chebe, mai shekaru 40 daga Sagagi da kuma Yakubu Abdulaziz, wanda ake kira Wawo, mai shekaru 21 daga Sabon Gida Sharada.

Yan sanda sun ce an cafke su ne a wani sumame da ya gudana daga karfe 10 na dare ranar 17 ga Janairu zuwa karfe 4 na asuba ranar 18 ga Janairu, 2026.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa Umar Auwalu, wanda ake zargin shi ne shugaban kungiyar kuma ɗan uwa ga marigayiyar, ya amsa laifin aikata kisan. Ya kara da cewa wanda ake zargin ya bayyana wa Yan sanda cewa su ne suka aikata wasu hare-hare da kashe-kashe a baya-bayan nan a wasu unguwannin Kano, ciki har da wani lamari a Tudun Yola.

Kisan Gillar Uromi: Iyalan Mafarautan Kano da Aka Hallaka A Edo Sun Fara Fidda Rai Da Adalci, Ƙungiyoyi Na Shirin Zanga-Zanga

Ya sandan Jihar Kano sun ce an kwato kayayyaki daga hannun wadanda ake zargin, ciki har da wasu tufafi masu dauke da tabon jini da wayoyin salula guda biyu na marigayiyar da adda da gora da kuma wasu kuɗaɗen da ake zargin an kwace a wurin da abin ya faru. Bincike na ci gaba domin gano karin bayanai da sauran waɗanda ke da hannu a lamarin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...