NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA
Daga Muazu Hardawa Bauchi
Tsohon Gwamnan jihar kaduna Malam Nasiru Ahmad Elrufai ya nemi kotu ta masa afuwar kan wasu kalamai da tsoffin lauyoyin sa na kariya suka yi a kotu yayin da ya ayyana sake shigar da sabbin takardun kara da bukatu a gaban kotun.
Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Babbar Kotun Kaduna ƙarƙashin jagorancin mai shari Darius Khobo ke ci gaba da sauraron ƙarar da hukumar ICPC ta gabatar tana tuhumar tsohon gwamna Nasir El-Rufai da zargin almundahanar kuɗaɗen gwamnati yayin da ya ke kan karagar mulkin jihar Kaduna.
A zaman kotun na Ranar Laraba 16/7/2026, Sabon lauyan da El-rufai ya ɗauka domin ba shi kariya Barrister Paul Erokoro yace jerin takardun guda uku da aka gabatarwa kotun kan buƙatar cike suke da kura-kurai, a don haka ya janye su, yana mai baiwa kotun haƙuri da neman afuwar ta, saboda laffuzan da akayi amfani da su a cikin takardun babu ko shakka ba su dace ba.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Read also: Kotu Ta Tabbatarwa ICPC Damar Bincikar Zargin Badaƙalar Tallafin Karatu A Kano
A don haka ya nemi kotun ta ba shi dama ya sake rubuta sabuwar takarda game da abin da suke buƙata daga kotun, kafin zuwa ranar 22 ga wannan wata da muke ciki na July.
Zargin rashin iya aiki da yinƙurin rashin adalci akan Alkalin kotun na daga cikin kalaman dake cikin takardun da tsohon lauyan na Malam Nasiru El-Rufa’i ya gabatar a baya, yana mai neman Babban Jojin Kaduna ya dauke shari’ar daga kotun sa.
Bayan fitowa Daga Zaman kotun, guda cikin lauyoyin hukumar ICPC, Barrister Ibrahim Mukhtar yayi karin haske ga manema labarai na sabon Lauyan El-Rufai ya shigar da buƙatar yin gyara a Shari’ar ran shida ga watan nan don haka yanzu an ɗage ƙarar zuwa ran 22/7/2026 kafin a kammala dukkan gyare-gyare da sabon Lauyan ke buƙatar yi sai a ci gaba da sauraron ci gaban Shari’ar.
Sai dai Sabon Lauyan da ke kare wanda ake ƙara Malam Nasiru El-Rufai, Mai Suna Barrister Paul Erokoro ya ƙi cewa komai yayin da manema labarai suka nemi jin ta bakin sa.
Tuni dai, Bangaren Masu ƙara, wato hukumar ICPC suka bayyana wa Kotu cewa sun kammala gabatar da shaidu da hujjojin su kan wanda suke ƙara a cewar Barrister Ibrahim Mukhtar.
Read also: ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Kano: An Soke Dokar Da Ta Kafa Hukumar KNUPDA – Majalisar Dokoki
Amma sai Barrister Ibrahim Mukhtar ya ce yawan maimaita bukatu da kuma rashin kammala takardun kariya daga bangaren wanda ake ƙara su ne ke haifar da tsaiko cikin shari’ar wadda a cikinta ake tuhumar tsohon Gwama El-Rufai kan wasu laifuka, kuma kotu za tai masa adalci, musamman suna buƙatar a yi zama a kan lokaci a yi hukunci a kan lokaci da zarar lauyan El-Rufai ya gama aiki game da gyaran Shari’ar da aka shigar.
Ƙarshe dai Alkalin kotun mai shari’a Darius Khobo ya dage sauraron shari’ar zuwa Ranar 22 ga watan Yuli na wannan shekara 2026.




























