ICPC Ta Kama Dan Jaridar Bisa Zargin Damfara Ta Naira Miliyoyin 14
Daga Sunusi K/Na’isa
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da hana almundahana ta Kasa (ICPC) ta ce ta shirya tsaf don gurfanar da wani ɗan Jarida mai suna Alkazim Kabir, wanda ake kira da Abbati Kabiru Abuwa, da ke Kano a gaban kotu, bisa zargin aikata laifin damfara da ta kai ta kimanin naira miliyan sha hudu.
Read also: NASIR EL-RUFAI YA NEMI AFUWA KAN KARAR DA ICPC TA SHIGAR A KANSA
A cewar sanarwar da mai magana da yawun hukumar, Demola Bakare ya fitar a yau Laraba, yace an yanke shawarar gurfanar da wanda ake zargin ne bayan karɓar korafe-korafe da dama daga jama’a, inda ake zarginsa da yin damfara, da yiwa jami’an gwamnati sojan gona da kuma yaudara.
Ga Wani Labarin:BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
Binciken hukumar ICPC ya gano cewa, Kabir ya sha yin sojan gona da sunan shi wani babban jami’an gwamnati ne ciki har da kiran kansa a matsayin hadiman shugaban ƙasa da mataimakin shugaban ƙasa, da kuma wasu ‘yan majalisar tarayya, domin damfarar mutane ta hanyar rabasu da maƙudan kuɗaɗe.
Read also: HUKUMAR ICPC TA GURFANAR DA LIKITAN NASIRU ELRUFAI A GABAN KOTU
Wanda ake zargin ya karɓi dala 3,300 da Riyal 1,620 daga wasu mutane biyu, inda ya bayyana musu cewa yana aiki a matsayin hadimin fadar shugaban ƙasa.
Hukumar ta kuma gano cewa wanda ake zargin ya ƙware wajen karɓar kuɗi da kaya ta hanyar zamba, musamman ta hanyar amfani da damar da ke tattare da shirye-shiryen tafiya zuwa ƙasashen waje domin ibada.
A lokacin da ya tafi aikin Umrah a ƙasar Saudiyya, ana zargin ya karɓi Riyal 11,000 daga wani abokin tafiyar sa, sannan daga baya ya tura masa da takardar bogi da nufin cewa ya biya bashin.
Ga Wani Labarin:GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
Read also: Ana Zargin Batagarin Matasa Da Bankawa Dubban Kaburbura Wuta A Makabartar Turum Dake Bauchi
Haka kuma, ya aika wa wani dillalin kula da masu tafiye-tafiye da takardar ƙarya ta canja wurin kuɗi na Naira miliyan 3 da dubu dari biyu wanda ya ce ya biya kuɗin jirgi, da otel da jirgin ƙasa.
Hukumar ICPC ta ce an riga an shigar da ƙarar wanda ake zargi a kotu, kuma za a gurfanar da shi gaban kotu mai hurumi nan bada jimawa ba, da zarar an sanya ranar zaman shari’ar.




























