BARAYI SUN GUNTULE HANNUN MATASHI A JIHAR KEBBI
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Wani matashi mai suna Auwal Auta Kardi, ya tsinci kansa cikin mummunan hali, bayan da wasu barayin mashin suk kai masa farmaki a daren Talatar da ta gabata kan hanyarsa ta komawa gida, ƙauyen Kardi dake cikin, Jihar Kebbi.
Bayanan da manema labarai suka samu ya nuna cewa barayin sun yi masa kwanton bauna tare da abka masa da sara da suka wanda har ya samu mummunan raunka daga karshe suka kwace masa mashin ɗin nasa, suka guntule masa hannun hagu tare da sassara shi a ka da sauran sassan jiki kafin su tsere.
Yanzu haka, Auwal na kwance a sashen gaggawa na Asibitin FMC Birnin Kebbi, inda yake karɓar kulawar likitoci a halin yanzu.
Read also: Yan Sanda Sun Kama Wand Ya ƙwaƙule Idon Kanwar Sa Da Kuma Bokan Da Ya bashi Sa’ar
Lamarin ya tayar da hankulan jama’a, inda ake kira ga ’yan siyasa, ’yan kasuwa, da masu hannu da shuni da su taimaka masa wajen samun jinya da lafiyar da ta dace, musamman ganin yadda ke da karamin karfi yana neman abinci ta hanyar aiki da mashin da wani ya ba shi yake lallaba rayuwa don ciyar da iyalansa.
Ga Wani Labarin:GWAMNATIN JIHAR BAUCHI TA SOKE TAKARDUN FILAYEN KIWO DA AKA RABAWA MANOMA A DARAZO
Da aka tuntubi rundunar ‘yan sanda ta jihar Kebbi sun bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike don gano wandanda suka aikata masa wannan mummunan aiki na rashin imani.
Haka kuma, al’umma sun bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa wajen dakile irin wadannan hare-hare da suka yi ƙamari a jihohin arewa, domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya.
Read also: Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
Ga Wani Labarin:WATA MATA TA KONE KANTA A BAUCHI SABODA BATA SAMU GANIN DIYAR FIRAYIM MINISTA BA
Haka kuma an bukaci Jama’a su taimaka wa hukumomin tsaro da addu’a tare da tona asirin miyagun mutane da aka san suna aikata irin waɗannan ayyukan rashin imani.



























