Yan Sanda Sun Kama Wand Ya ƙwaƙwule Idon Kanwar Sa Da Kuma Bokan Da Ya bashi Sa’ar
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Bayan afkuwar wani lamari mai tayar da hankali da ya faru a wani kauye da ke kusa da garin Wailo, a ƙaramar hukumar Ganjuwa ta jihar Bauchi, inda wani matashi Auwalu ya ƙwaƙwule idon ƙanwarsa yar shekara 7 don neman biyan bukatarsa ta duniya, rundunar Yan sanda ta cika hannu da mutumin da wanda ya sa shi kawo masa idon domin yin tsari.
Da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, mahaifin yarinyar, Malam Muhammad Adamu, ya bayyana cewa wanda ake zargin ɗan uwanta ne na jini amma ya ci amanar su ta hanyar yaudarar yarinyar yadda ya aikata mata wannan ta’annati.
Ya ce Auwalu ya ja ƙanwarsa cikin daji bisa yaudara kafin ya aikata mata wannan mummunan aiki da ya bar ta da raunuka masu tsanani a idanuwanta biyu da ya ƙwaƙwule.
Read also: Tsaro: Hukumar Yan sanda ta Haramta Yin Wasan Tashe
Ga Wani Labarin:Jita-Jitar Juyin Mulki Ba Gaskiya Bane Kuma Makirci Ne — Shelkwatar Tsaro
Bayan ashirin sa ya tonu an garzaya da Ruƙayya asibitin koyarwa na ATBUTH da ke Bauchi inda likitocin ido suka yi mata aiki don gyara wajen raunukan mazaunan idanuwan biyu.
Babban likitan asibitin ido na ATBUTH, Dr. Shahir Bello Umar, ƙwararren likitan ido yace ganinta ba zai sake dawo ba lamarin da ke nufin ta makance gaba ɗaya saboda ya lalata dukkan idon biyu.
Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaye sunansa ya tabbatarwa wa manema labarai cewa tuni jami’an tsaro suka kama wanda ake zargi da aikata laifin, harma da wanda ake zargin shi ya saka shi ya nemo idon don aikata ayyukan tsafi.
Read also: Jami’an Tsaro Sun Yi Arangama Da Al’ummar Gari A Garko Har An Kone Motar ‘Yan Sanda
Ga Wani Labarin:Babu Bukatar Lissafi Don Shiga Tsarin Koyon Arts da Humanities – Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Bauchi CSP Mohammed Ahmed Wakil ya tabbatar da abkuwar lamarin. Kuma kwamishinan Yan sanda na jihar Bauchi CP Omolarin Aliyu ya bayar da umarnin ci gaba da bincike don gurfanar da masu laifin a gaban kotu.



























