Connect with us

Hi, what are you looking for?

Ilimi

Babu Bukatar Lissafi Don Shiga Tsarin Koyon Arts da Humanities – Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana

Dr. Tunji Alausa
Dr. Tunji Alausa

Babu Bukatar Lissafi Don Shiga Tsarin Koyon Arts da Humanities – Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana
Daga Adita

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar da sabon tsarin manufofi da ke sauya yadda ake karɓar ɗalibai, inda ta bayyana cewa daga yanzu ɗaliban da ke neman shiga shirye-shiryen Arts da Humanities a jami’o’i da kwalejojin fasaha (polytechnics) na Najeriya ba lallai ne su sami credit a Lissafi (Mathematics) a jarrabawar SSCE ba.

Sanarwar ta fito ne a wata takarda da mai magana da yawun ma’aikatar, Folasade Boriowo, ta fitar a ranar Talata, 14 ga Oktoba, a birnin Abuja.

A cewar sanarwar, sabon tsarin ya shafi ɗaliban da ke rubuta jarrabawar WAEC da NECO.
Ga Wani Labarin:Daliban Jami’ar Aliko Dangote dake Wudil sun Karrama Shugaban Hukumar Karota

A baya, duk wanda ke neman shiga kowane fanni na karatu, dole ne ya samu akalla credits biyar wanda suka haɗa da Turanci da Lissafi, kafin a ba shi damar shiga makarantar gaba da sakandare.

Sai dai bisa wannan sabon tsari, Lissafi ba zai sake zama dole ba ga waɗanda ke neman shiga fannoni na Arts da Humanities.

Sanarwar ta ƙara da cewa:

“Sabon tsarin ƙasa na sharuɗɗan shiga manyan makarantu an tsara shi ne domin kawar da shingaye ba tare da rage ingancin ilimi ba. Wannan sauyi na nufin samar da daidaito da sauƙaƙe damar shiga bisa bukatun kowanne fanni na karatu.”

“Sabon tsarin ya shafi jami’o’i, kwalejojin fasaha (polytechnics), kwalejojin ilimi (colleges of education), da Innovation Enterprise Academies a fadin ƙasar kamar haka:”

Jami’o’i:
Akalla credits biyar (5) a darussa masu dacewa, ciki har da Turanci, a zama biyu (2) kawai. Lissafi dole ne ga fannoni na Kimiyya, Fasaha, da Zamantakewa (Social Sciences).

Kwalejojin Fasaha (ND Level):
Akalla credits huɗu (4) a darussa masu dacewa, ciki har da Turanci ga fannoni marasa alaƙa da kimiyya, yayin da Lissafi yake zama dole ga shirye-shiryen da suka danganci kimiyya.

Kwalejojin Fasaha (HND Level):
Akalla credits biyar (5) a darussa masu dacewa, ciki har da Turanci da Lissafi.

Kwalejojin Ilimi (NCE Level):
Akalla credits huɗu (4) a darussa masu dacewa, inda Turanci yake zama dole ga fannoni na Arts da Social Sciences, yayin da Lissafi yake zama dole ga Kimiyya, Sana’a, da Fannin Fasaha (Technical).

Ga Wani Labarin:Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun 8 masu zaman kansu

Ma’aikatar ta bayyana cewa wannan mataki na nufin kawar da wasu shingaye marasa amfani ga ɗalibai tare da tabbatar da tsarin karɓar ɗalibai mai adalci da haɗin kai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...