Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Malam Mador / Kaugama Ya Raba Tallafin Karatu Ga Ɗalibai 500
Daga Sunusi K /Naisa
Read also: Babu Bukatar Lissafi Don Shiga Tsarin Koyon Arts da Humanities – Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana
Ɗan Majalisa mai wakilta Malam Madori da Kaugama a jihar Jigawa Hon. Abubakar Makki Yalleman ya kaddamar da rabon kayyan tallafin karatu ga ɗalibai 500 da suka fito daga mazabu Ashirin da biyu(22) dake ƙarƙashin ƙananan hukumomin Malam Madori da Kaugama da ke jihar Jigawa.
Da yake rabon kayyan a madadin Ɗan Majalisar, Shugaban Kwamitin ilimi, Maiunguwa Ibrahim Zakar Al-kampaly, ya ce ɗalibai 500 ne suka amfana da shirin, kuma an zakulo su daga mazabu 22 na ƙananan hukumomi Malam Madori da Ƙaugama.

Read also: Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi
Shugaban ya ce yana daga cikin alƙawarin da Dan Majalisa ya yi na taimakawa ɗalibai da farfaɗo da ilimi a ƙananan hukumomin.
Kayan Makarantar da a ka raba sun haɗar da jakankuna, littaafai, tebura, kujeru da kayan makaranta (uniform).
Shugaban kwamitin (Makki Educational Support Program)l, MESP), Maiunguwa, Ibrahim Al-kampaly ya godewa Dan Majalisa Makki da wanna abin alheri da ya yi, ya ce kwamitin su zai ci gaba da bawa ilimi fifikon da ya kama ce shi domin ceto ilmin da ga durkushewa.
Shugaban ya roki mawadata da ‘yan siyasa da kuma masu riƙe da madafun iko da su yi koyi da Ɗan Majalisar Malam Madori da Ƙaugama Hon. Makki Yalleman a ƙoƙarin sa na bunƙasa ilimi a jihar Jigawa baki ɗaya.
Ya ja hankalin wadanda suka rabauta da kayan da su yi amfani da su kamar yadda ya dace.
Da yake jawabi, Dokajin Hadejia, Hakimin Malam Madori, ya yabawa Hon. Abubakar bisa kishin sa na ciyar da ilimi gaba ya kuma buƙaci iyaye da su mai da hankali ga ilimin ‘yayensu.
Wazirin Ningi Ya Yi Murabus, Sakamakon Tsoma Siyasa a Harkokin Masarautar Ningi
Taron ya samu hadartar manyan mutane wanda suka haɗar da Wakilin Chairman MMR (Speaker MMR) da Tsohon Kantomar mulki, Alhaji Ya’u Sakatare da Tsohon Mataimakin Shugaban Karamar hukuma, Alhaji Ahmed Mairakumi da Dokajin Hadejia, Hakimin Malam Madori da S.A Higher Education, A.U Dunaru da sauran su.



























