Aƙalla Ɗalibai Mata Dubu 12,133 Zasu Sami Tallafin Karatu Na AGILE A Bauchi
Daga Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Ɗan Majalisar Tarayya Mai Wakiltar Malam Mador / Kaugama Ya Raba Tallafin Karatu Ga Ɗalibai 500
Read also: Kyautata Zamantakewar Aure: Kungiyar Anwarul-Qalam Bauchi ta Horas da ‘Yan Mata 100
A ƙoƙarin gwamnatin tarayya da haɗin gwiwa da shirin AGILE na dakele yawaitar cire yara daga makarantun gaba da firamare, yara mata dubu 12, 133 sun fara cin gajiyar shirin tallafi karatu na Naira dubu 40 ko waccen su a jihar Bauchi.
Shirin zai taimakawa yara mata wajen sauƙin zuwa makaranta a maimakon yawan tallace-tallace da iyaye kan dora musu domin samun abin masarufi na yau da kullum.
Hajiya Ladi Hamma Mohammed jagorar Shirin a jihar Bauchi ita ta bayyana haka a taron manema labarai da ta kira, ta ce a farkon shirin AGILE sun ɗauki sunayen yara sama da dubu 20 suka tura wa Bankin Duniya (World Bank), domin tantancewa da nufin basu tallafin karatu.
Shugabar ta ce a karon farko sun samu yawan yara dubu 18,368 da aka tantance aka kuma sake mayar da sunayen su aka kara tantancewa aka dawo da sunayen yara dubu 12,133, a in da aka yadda su fara tura musu kuɗin tallafin karatun kafin a sake tantance sauran sama da yara dubu biyar.
Kwankwaso Ya Bada Sabbin Muƙamai Ga Kwamishinonin da Suka Bar Kujerunsu Don Ɗabbaƙa Shahadar Kwankwasiyya
Hajiya Ladi Hamma ta ce amma dalibai na gaba ba za su ci moriyar tallafi naira dubu 40 kamar na farko ba, amma za a ba su naira dubu goma ko wacce a ko wane zangon karatu.
Ta kara da cewa don a basu karfin guiwa kan zuwa makarantar kowace daliba ana son ta samu kashi 70 cikin dari na halartar zuwanta makarantar.
Ta ce Bankin Duniya suna da tsari wajen tantance daliban, don haka yaran da basu samu shiga ba yawancin su ba su da katin shaidar dan kasa wato lambar NIMC sai daga baya suka yi.
Har su kan su iyayen yaran dole sai sun kawo NIMC lambar zama dan kasa, wasu kuma an yi ta samun banbanci ko shigar da bayanai ba daidaiba shima ya kawo tsaiko.
Bayan haka akwai matsalar da aka fiskanta wacce ta shafi sunan iyaye da masu lura da yaran ko banbancin masu rike da yaran da a duk lokacin da aka samu banbancin bayani dole a nemi tantancewa ta hanyar gyara suna don ya koma kan tsarin bayanai na gaskiya.
Har wa yau game da batun da ake yi na za a gina sabbin makarantu a cikin shirin AGILE amma har yanzu ba a gina ba har shekara biyu. Ta ce akwai tsare tsaren da ake bi masu yawa kuma sun yi duk gyaran da ya kamata sun tura zuwa bankin duniya da hukumomin da suka dace. Idan sun amince an dawo da su sai a fara saka Tanda don yan kwangila su fito su nemi ayyukan a basu kwangilolin kamar yadda aka shirya za a gyara makarantu sama da guda dubu.
Hajiya Ladi Hamma ta ce dukkan ayyukan gine gine da gyaran makarantu aikin yana bukatar kwararru su gudanar kuma yanzu ana ta musu bita da taron horaswa duk lokacin da aka gama horas da mutane 156 masu aikin za su sanar da duniya a duk lokacin da aka shirya taron horaswan.
Bayan haka ta bayyana cewa dalibai dubu 12,133 da aka tantance kowace ta samu taimakon naira dubu 40 Wanda ya kunshi kudin rijistar da sauran kudin kayan aikin makaranta na kowace daliba Yar aji daya a karamar Sakandare da Aji daya a babbar Sakandare wanda yanzu haka sun shiga ajin gaba dukkan su.
Ta kara da cewa haka Shirin zai gudana a kowane zangon karatu, Kuma za a ba daliba naira dubu goma har ta kammala karatun ta yadda a shekarar farko daliba Za ta samu naira dubu 60 a shekara ta biyu Za ta samu dubu 30 haka a shekara ta uku Za a bata naira dubu 30 jimla ta zamo naira dubu Dari.
Daga karshe ta Kara da cewa akwai makarantun Matan aure guda 22 da ake da dalibai sama da dubu daya da za a fara Koya musu sana’a na tsawon watanni uku zuwa wata tara don su dogara da kan su.
Game kuma da maganar da ake yayatawa ta jita jitar cewa bayan dalibai sun gama karatu Za a ba su kyautar waya ta naira dubu dari don aiki da ita a manyan makarantu, tace wannan ba gaskiya bane labari ne na kanzon kurege.
Don haka sun bayyana rashin jin dadin su game da wasu dabiu da wayar hannu ta haifar a cikin al’umma.
Kwararriyar Mai Karanta Labarai Lami Maccido Ta Rasu Tana da Shekara 72
Don haka ta bukaci iyayen yara su kwantar da hankalin su wannan magana karya ce suma haka suke jin ta.
Hajiya Ladi Hamma ta ja hankalin iyaye su bayar da goyon baya ga dalibai ta hanyar yin aiki da kudin tallafin don inganta karatun su ta yadda za su zamo abin alfahari ga kasa da Jama’a.



























