Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Kwararriyar Mai Karanta Labarai Lami Maccido Ta Rasu Tana da Shekara 72

Hajiya Lami Maccido
Hajiya Lami Maccido

Kwararriyar Mai Karanta Labarai Lami Maccido Ta Rasu Tana da Shekara 72

Daga Sunusi K/Naisa

Kwararriyar mai karanta labarai, Hajiya Lami Hafsat Maccido, wadda aka san ta a matsayin mace ta farko ‘yar asalin ƙasar nan da ta fara gabatar da shirye-shirye a Radiyon Kano, kuma tana cikin mutanen farko da suka fara bayyana a allon talabijin na NTA Kano da CTV 67 a shekarun kafuwarsu, ta rasu tana da shekara 72.

Jaridar KANO FOCUS ta bayyana cewa fitacciyar mai watsa labaran ta rasu ne a daren Talata bayan gajeriyar rashin lafiya. An sanar da rasuwarta ne ta cikin wani saƙo da Injiniya Abubakar Garba Maccido ya yaɗa a WhatsApp.

Ana girmama Hajiya Lami Maccido sosai saboda rawar gani da ta taka a fagen yaɗa labarai a Arewacin Nijeriya, inda muryarta da kasancewarta suka taimaka wajen gina tsarin gabatar da shirye-shiryen radiyo da talabijin na farko a Kano. Rasuwarta na tabbatar da ƙarshen rayuwarta, wanda hakan ya sanya abokan aikinta da masoya da kuma al’umma suke ta miƙa ta’aziyya tare da tuna sadaukarwarta, da ƙwarewarta da gudummawar da ta bayar wajen bunƙasa harkar watsa labarai a jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Kaɗu Matuƙa Da Rasuwar Ƴan Jarida Sakamakon Hatsarin Mota

An haifi Maccido a ranar 12 ga Agusta, 1954. a Jos, Jihar Filato, daga mahaifi wanda Asalinsa ɗan jihar Borno ne da kuma mahaifiyarta Bafulatana daga Jihar Katsina.

Ta yi karatun firamare a Makarantar Township Primary School, sannan ta halarci makarantar sakandare ta St. Louis Secondary School, duka a Jos, kafin ta wuce ABC/ABU Kano domin karatun gaba da sakandare.

Maccido ta fara aiki a matsayin mai karɓar kuɗi a Sheshe Departmental Stores da ke Kano, kafin ta fara aiki da Radiyon Kano a shekarar 1974, inda ta yi aiki har zuwa 1976. Daga bisani ta koma Hukumar Talabijin ta Nijeriya (NTA) Kano-wadda a wancan lokaci ake kira NTV Kano-inda ta yi aiki daga 1976 zuwa 1981.

Daga baya ta koma CTV 67 a matsayin ɗaya daga cikin ma’aikatan farko na kafuwar tashar. Ta yi ritaya a shekarar 2012 bayan shafe shekaru 35 tana hidima mai cike da sadaukarwa a fagen yaɗa labarai.

Maccido, tare da tsoffin abokan aikinta Dr. Faruk Umar Usman, Alhaji Ishaq Hadeijia, da Alhaji Wada Abdullahi Kachako, sun taka muhimmiyar rawa wajen sanya wa tashar suna CTV 67 (Community Television) lokacin da aka kafa ta a zamanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Abubakar Rimi.

Huɗuba: Babu Dabara Ka Ɓoye Kayyan Masarufi, Kuma Ka Biya wa Wasu Aikin Umarah, In Ji Liman Nura Ishaq

Rasuwarta ta janyo ɗimbin saƙonnin ta’aziyya daga ‘yan jarida, tsoffin abokan aiki da masoya, inda da dama suka bayyana ta a matsayin jagora bar koyi, ƙwararriyar ma’aikaciya, kuma fitacciya da nagarta a harkar yaɗa labarai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...