Amurka ta gargadi ‘yan ƙasarta su ƙauracewa gine-ginen gwamnati da kuma sashin da sojoji suke a Abuja
Daga Sani Aminu
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya ya fitar da wata sabuwar sanarwa game da harkokin tsaro, inda ta gargadi ‘yan Amurkan da su ƙauracewa duk wata ziyara da ba ta da mahimmanci a gine-ginen gwamnati da cibiyoyin soji a babban birnin tarayya Abuja dake Najeriya.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Sanarwar da aka fitar a ranar Litinin, ba ta yi nuni da wata takamaimiyar barazana ba, amma an fitar da ita ne a cikin yanayin da ake ciki na tabarbarewar tsaro a duniya da kuma tashe-tashen hankula na siyasa a yankuna da dama.
Karanta kuma:Mutane 5 sun mutu da yawa sun jikanta sakamakon fashewar bom a Kano
“Ofishin jakadancin Amurka ya ce zasu cigaba da sa ido sosai kan lamarin kuma ya ba da shawarar cewa ‘yan Amurkan su guji ziyartar gine-ginen gwamnati da wuraren soji da ke Abuja har sai an samu wata sanarwar anan gaba,” in ji ofishin a cikin sanarwar da ta fitar.
Fadakarwar ta yi kira ga ‘yan ƙasar Amurka da ke zaune ko kuma masu balaguro a Najeriya da su kasance a faɗake da sabunta tsare-tsaren tafiye-tafiyensu, da kuma saurarar labarun cikin gida da tashohin gwamnatin Najeriya.
Read also: Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Dangane da irin wannan gargadin daga wasu gwamnatocin ƙasashen yammacin duniya, sanawar ta ce akwai buƙatar ƙara wayar da kan al’umma.
Karanta kuma:Da ɗumi-ɗumi: Minista Wike ya ce masu ido da kwalli sune matsalar Abuja
Ofishin Jakadancin na Amurka ya kuma tunatar da ‘yan ƙasarta ƙa’idodin balaguron da ake da su tare da ƙarfafa yin rajista tare da Shirin Rijistar Matafiya (STEP) don tabbatar da sun sami sabbin abubuwan sabunta tsaro da tallafin gaggawa.



























