Minista Wike ya ce masu ido da kwalli sune matsalar Abuja
Daga
Read also: Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta Faranta Zukatan Tsofaffin Abokan Aikinta Na AKTH
Sunusi K/Na’isa
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, ya ce manyan mutane da ke zaune a Abuja sune matsala ta fuskar ƙin biyan haraji da kuɗin kasa (ground rent). Ya bayyana haka ne yayin kaddamar da titi mai suna Zakari A. Kyari Street wanda ya taso daga unguwar Mabushi zuwa Katampe, da Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar domin cika shekaru biyu a mulki.
Wike ya ƙara da faɗin manyan mutane ba sa son biyan haraji a Abuja, amma suna biyan haraji da kuɗin ƙasa (ground rent) a London da Amurka. Ya bayyana cewa titin da aka ƙaddamar yau da sauran hanyoyi an gina su da haraji da masu biyayya suka biya.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
A cewar shi, ” ba talaka ke gina gida a Katampe da Mabushi ba. Masu kuɗi ne ke gina gidajen, don haka dole su biya haraji domin ci gaba”. Inji Wike.
A Iya Karanta Wanna:Hanyar Dan Madanho ta gagari Kundila, mazauna yankin na roƙon Gwmna Abba ya kawo ɗauki
Babban Ministan ya ce Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja na samun kashi 1% na kudin da gwamnatin tarayya ke samu, wanda ba ya wadatar da biyan albashi da ayyuka. Ya jaddada cewa ba za a iya jin daɗin ababen more rayuwa ba ba tare da biyan haraji ba, kuma bai shafi jam’iyya ba.
Ya bukaci Shugaba Tinubu, wanda Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Benjamin Kalu ya wakilta, da ya ja hankalin mazauna Abuja su riƙa biyan haraji. Ya kuma ce duk wanda ke da fili amma bai biya kuɗin kasa ba, za a wallafa sunansa a jarida domin duniya ta shaida.
A Iya Karanta Wanna:Yarjejeniyar Zaman Lafiya da Alero: Gaskiya Ko Wasan Kwaikwayo Da Rayukan Al’umma
Ya kuma jaddada goyon baya ga gwamnatin tarayya da take Ƙoƙarin inganta rayuwar mazauna Abuja da kewaye.




























