DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)
Daga Yazid Sunusi Yahaya
Read also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2)
Idan ba a manta ba mun tsaya akan tsabtar wurin kiwon, Kuma inshallah za mu ɗora da muhimmin al’amari a cikin tukuna kiwo, musamman kiwan kaji wato samar da cimaka.
ABINCI KO DUSA
A kiwon kaji abu mafi muhimmanci shine ‘DUSA’ ko abincin kaji wanda a duk kuɗaɗen da ake kashewa wajen kiwo yake ɗaukan kaso mafi girma kwatankwacin 55-60% na gaba ɗayan kudin gudanarwar.
Dusar kaji ta kasu kala- kala kuma kowace da akwai dalilin da yasa aka samar da ita ko amfaninta. Amma mu anan munfi amfani da guda biyu wato PELLETS da kuma CRUMBLESS (Bansan yadda zan fassararsu da Hausa ba) Pellets: dai tafi amfani ga manyan kaji musamman masu kwai ko wadanda suka tasa saboda karancin (protein contents) da ake sanya mata.
Read also: DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Crumbles: Ita kuma wannan kalar dusar tana ɗauke da (protein contents) mai yawa wanda ita ce mafi kyau ga kiwon kaji musamman masu bayar da nama wato (Broilers). Duk da akan yi amfani da Pellets ga Broilers ɗin amma musamman a lokacin zafi saboda sauƙin samun protein a jikin su, yin hakan yana taimakawa wajen daidaita zafin jikin kajin. Haka kuma Crumbles an so a yi amfani da ita lokacin sanyi domin ta taimaka wajen daga zafin jikin kaji.
A Karanta:DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2)
A kiwon kaji ‘DUSA’ tana da mutukar amfani ga kaji da sauran tsuntsaye domin tana taimakawa sosai wajen girman kaji tare da inganta lafiyar su, hakan shine babbar riba ga mai kiwo Kuma akasin haka kan janyo lalacewar kaji ko da sun girma ne sukan ɗauke su zama babu wadattaccen nama a jikin su, hakan kuma kan haddasa asara ga mai kiwo, canja wa kaji dusa daga wani kamfani zuwa wani babbar matsalar ga kaji. Shawara ga mai kiwo shine ya tabbatar ya samu kaso sabain (70%), na dusar da zai kiwo ta kamfani ɗaya ce har sanda za’a fitar dasu (A saida).

Kaji
A matakin farko wato (Day-old stage): kaji na bukatar dusar da ake kira da (STARTER FEEDS), wannan dusar tana dauke da sinadaran protein mai yawa aciki don taimakon su Kajin su sami saurin girma da buɗewa, kuma tana ɗauke da sinadarin da zasu ƙara lafiyar garkuwar jikinsu, don haka ake bukatar dusar ta kasance daga kamfani mai Inganci. Za a iya basu wannan dusar har tsawon sati 3-4 babu laifi musamman ga kaji (Broilers), wasu Kuma har a gama kiwo tsawon sati biyar zuwa sama babu laifi akan haka.
A Karanta:DABARUN KIWON KAJI A LOKACIN YANAYIN SANYI (1)
Zan dora inshallah zuwa kashi na gaba.
Yazid Sunusi Yahaya, marubuci daga unguwar Kofar naisa a jihar Kano Nijeriya.
#stentornews
#yazeedpoultryfarmer
#eachoneteachone




























