Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Dalibai a Ingila ba za su samu damar amfani da wayoyinsu na hannu a kowane lokaci cikin yini ba, sakamakon sabbin tsauraran dokokin da gwamnatin kasar ta fitar.
Sabuwar dokar da ta fara aiki a watan Yuni ta ɗora wa makarantu da hukumomin kula da makarantu alhakin tabbatar da cewa babu amfani da wayoyin hannu a duk tsawon lokacin da ake gudanar da karatu. Yanzu dai ministocin ƙasar sun ce za a ƙara tsaurara dokar, ta yadda za ta wuce tsarin da wasu makarantu ke amfani da shi na cewa, “kar a gani, kar a ji”, inda ake barin ɗalibai su ajiye wayoyinsu a cikin jakunkunansu muddin ba a ganinsu kuma ba a jin sautinsu.
Read also: JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Sai dai ƙungiyoyin shugabannin makarantu sun yi gargaɗin cewa makarantu za su fuskanci matsaloli wajen aiwatar da sabbin dokokin ba tare da ƙarin tallafin kudi daga gwamnati ba.
Sakatariyar Ilimi ta ƙasar, Lucy Powell, ta ce saƙon da gwamnati ke son isar wa iyaye da ɗalibai a bayyane yake, wato “makaranta wajen neman ilimi da kulla abota ne, ba wajen yawan kallon wayoyi ba.”
Gwamnatin ta bayyana cewa bai wa ɗalibai damar amfani da wayoyin hannu na iya ɗauke hankalinsu daga karatu da kuma mu’amala da sauran ɗalibai.
Read also: Tsaro: Hukumar Yan sanda ta Haramta Yin Wasan Tashe
Makarantu ne za su yanke shawarar yadda za su aiwatar da wannan doka. Wasu sun zuba jari wajen samar da jakunkuna na musamman masu kulle wayoyi ko kuma kaba wa masu tsaro, yayin da wasu ke karbar wayoyin ɗalibai a farkon ranar karatu ko kuma hana shigarsu makaranta da ko harabar makarantar da wayoyi baki ɗaya.
Da take zantawa da shirin BBC Breakfast, Powell ta ce irin waɗannan matakai za su iya haifar da “sauyin al’adar gudanar da makaranta baki ɗaya”, wanda ta ce shi ne abin da gwamnati ke son ganin ya zama ruwan dare a dukkan makarantu.
Karl Harrison, shugaban makarantar yara maza ta Burnage Academy da ke Manchester, ya shaida wa shirin cewa makarantar ta kashe fam 20,000 wajen samar da na’urorin gano karafa da kuma jakunkuna na musamman da ake kulle wayoyin hannu a cikinsu.
Ya ce duk da cewa wasu ɗalibai na ganin an tauye musu ‘yancinsu, kulle wayoyin ya taimaka wajen ƙara cuɗanya da mu’amala tsakanin ɗalibai a makarantar.
Ya ce: “A yanzu ɗalibai suna iya tattaunawa da juna, maimakon su riƙa kallon wayoyinsu. Haka kuma, hakan ya ƙara inganta mayar da hankali a lokacin darussa saboda an rage abubuwan da ke ɗauke hankali, lamarin da ya sa ɗalibai ke samun maki mafi girma a yanzu.”




























