Ebola Ka Iya Hadasa Ɗage Zaɓen 2027 A Najeriya
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: An Buƙaci Mutane Su Fito Gwajin Hawan Jini da Ciwon Siga
Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa (NCDC),Jide Idris, ya ce za a iya samu cikas tare da ɗage babban zaɓen shekarar 2027, idan ɓarkewar cutar Ebola ta yaɗu a Najeriya zuwa matakin da zai iya sanya gudanar da zaɓen cikin haɗari.
Darakta-Janar na hukumar, ne ya bayyana hakan yayin wata hira da shi a gidan talabijin na Channels TV, inda aka tattauna kan ɓarkewar cutar a wasu sassan ƙasar.
Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Read also: Kasar Saudiya ta Jibinci Gabarar Raba Tagwayen da Aka Haifa a Manne
Sai dai Idris ya jaddada cewa a halin yanzu babu buƙatar ɗage zaɓen, yana mai fatan cewa lamarin ba zai taɓarɓare har ya kai ga hakan ba, tare da bada tabbacin hukuma na dakele yaɗuwar cutar.
Kamar yadda aka sani ne, an tsara fara babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027 a watan Janairu, yayin da jam’iyyun siyasa da masu neman takara suka fara bazama domin yaɗa manufa don shirye-shiryen tunkarar zaɓen.
Shugaban NCDC yace sun daɗe suna sanya ido kan halin da ɓarkewar cutar Ebola take ciki musamman a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), kafin ɓullarta a Najeriya.
Ya ƙara da cewa hukumomin lafiya sun yi hasashen yiwuwar cutar ta shigo Najeriya saboda yawan zirga-zirgar jama’a tsakanin ƙasashen.
Read also: Ranar Shanyewar Barin Jiki Ta Duniya: Ko Me Ke Kawo Cutar?
“Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya
Haka kuma, shugaban NCDC ya yi watsi da yiwuwar amfani da ɓarkewar cutar a matsayin siyasa, yana mai cewa bai kamata a mayar da matsalolin lafiya wata hanya ta cimma muradun siyasa ba.




























