Connect with us

Hi, what are you looking for?

Lafiya

Kasar Saudiya ta Jibinci Gabarar Raba Tagwayen da Aka Haifa a Manne

Conjoined Twins
Conjoined Twins

Daga SA K/Na’isa

Gidauniyar Jin Kai ta Sarki Salman da ke Saudi Arebiya (KSARelief) ta dauki nauyin yi wa ‘yan tagwayen da aka haifa a jihar Kano a hade aiki a can asibitin Sarki Abdulaziz a kasar ta Saudiya kyauta.

Kamar yadda mai magana da ofishin jakadanci na Saudiyya da ke Najeriya Alsahabi ya fada, a lokacin da ake kokarin fitar da yaran zuwa Saudiyya.

Labarin Hassan da Hasana Isa Hassan ya mamaye kafofin yada labarai na gida da waje, wannan shi ya ba da damar har wannan gidauniya ta samu ikon kawo agaji domin ceto mannanun ‘yan tagwayen don ceto lafiyarsu da kuma samun damar rayuwa kamar yadda sauran mutane ke yi kamar yadda Kamfanin Dillacin Labarai na kasar nan (NAN) ya wallafa.

Kamfanin Dillacin Labarai na NAN ya ce an haifi ‘yan tagwayen a manne inda kusan dukkan jikinsu a hade yake, ban da kawunansu, wanda tabbas aikin raba su sai kwararun likitoci.

Labarin wadanan tagwaye, ya taba zuciyar miliyoyin al’ummar duniya, don haka aka ja hankalin kwararru domin kawo agaji ga wadannan mannanu tagwaye.

Aikin raba tagwayen za ayi shi a Babban Asibitin Sarki Abdulaziz da ke Riyadh, kuma zai shiga cikin tarihin aiki mafi girma da daukar hankali da wannan cibiya za ta gudanar.

Abba

Abba

“Shi dai wannan aikin raba tagwayen zai kunshi duk wasu kwararrun likitoci na fannoni daban-daban, musamman likitocin fannin lafiyar yara da masu jinya da makamantasu domin samun nasara”, in ji wani kwararren likita.

Haka kuma, za a tabbatar an ba wa iyayen yaran dukkan kulawar da ta kamata, da suka hadar da makwanci da abinci da sauran bukatu a birnin na Riyadh.

Ya ce Saudi Arebiya ta na ba da cikakkiyar kulawa ga fannin lafiya ga kasashe da dama musamman irin wannan aiki na raba hadadun tagwaye.

Ita wannan cibiyar samar da lafiya ta Sarki Salman an samar da ita a shekarar 2015. Ta kai dauki ga kasashe 94 a fiye da ayyukan samar da lafiya 2,500 ya zuwa yanzu.

Kawo wannan lokaci an gudanar da aikin raba mannannun tagwaye har guda 133 wadanda aka turo su daga kasashe 24, kuma an sami nasarar aikin guda 59 daga cikin wannan adadi.

Da yake bankwana da jariran a filin tashi da sauka na Mallam Aminu Kano, Gwamna Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya yi addu’ar samun nasarar akin gami da gode wa Cibiyar Sarki Salman da kuma kasar Saudiyya bisa wannan gudummawa da suke bayarwa.

Gwamna Abba ya ce kafin tashin mannannun tagwayen, an kula da lafiyarsu a Asibitin Nasarawa da ke birnin Kano.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...