Gwamnatin Tarayya ta Rage Kuɗin Wankin Koda Zuwa ₦12,000 daga ₦50,000
Daga Adita
Read also: Gwamnatin Tarayya Haɗin Gwiwa da Bauchi Sun Samar da Motocin Daukar Marasa Lafiya Kyauta
A ƙoƙarin sa na taimaka wa majiyata masu fama da larurar ciwan koda, Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da bayar da tallafin gwamnati kan aikin wankin koda ga ƴan Najeriya a asibitoci goma sha ɗaya (11), a inda ya rage kuɗin daga Naira dubu 50 zuwa Naira dubu 12,000.
Ana aiwatar da tallafin ne a duk shiyoyi shida na ƙasar nan a wasu asibitocin gwamnatin tarayya.
Asibitocin da aka yi ragin sun haɗar da Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Tarayya (FMCs) Ebute-Metta Legas, Jabi, Abuja, Asibitin Kwalejin Jami’ar Ibadan (UCH), Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Owerri, da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH) Maiduguri.
Read also: Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
A Karanta Wanna:Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Sauran su ne Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Abeokuta, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Legas (LUTH) Legas, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) Azare, Asibitin Koyarwa na Jami’ar Benin (UBTH) Benin, da Jami’ar Koyarwa ta Calabar (UCTH) Calabar.
An kaddamar da tallafin ne a watan Janairu a asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.
Read also: Ebola Ka Iya Hadasa Ɗage Zaɓen 2027 A Najeriya
A Karanta Wannan:Mun Fasara Littafin Sunayen Ma’aikatu Da Hausa, Don Saukakawa Abokan Aiki – Dan jarida Muhammad
A cewar Hammatu Haruna, Manaja mai kula da sashen masu ciwon ƙoda a asibitin koyarwar na Bauchi, tallafin zai kawo sauki ga marasa lafiya, musamman masu ciwon ƙoda, idan akai la’akari da makudan Kuɗaɗen da suke kashewa.
BizPoint




























