Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Daga Sunusi Kofarnaisa
Read also: Kotu ta Umarci Masu Barkwanci Na TikTok A Kano Dasu Yi Aure Bayan Yaɗa Bidiyon “Futsara”
Wata kotun Majistiri a Jahar Kano da ke zaune a gini mai lamba 47 a unguwar Norman’s land a ƙaramar hukumar Fagge ta aike da wasu ƴan TikTok su biyu gidan yari na tsawon shekara guda amma da zaɓin tara tun bayan karar da Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano ta shiga dasu kan zargin yada futsara a kafafen sada zumunta na zamani domin girbar abinda suka shuka.
A Karanta Wanna:DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)
Kotun ta samu ƴan TikTok ɗin biyu da laifin wallafa wasu bidiyoyi na rashin ɗa’a waɗanda suka ci karo da addini da kuma tarbiyyar malam Bahaushe tare da dokokin da suka kafa Hukumar ta tace fina-finai ta Jahar Kano.
Read also: Kotun Kano Ta Yanke Wa Mutum Biyu Hukuncin Kisa Sau Bakwai Kowanne Saboda Kashe Mace Da Yara Shida
A Karanta Wanna:Addu’ar Magabata ita ce Sirin Samun Zaman Lafiya a Mararabar Gurku, Inji Sarkin Hausawa Mani
Tun farko hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dau tsawon lokuta domin ganin yadda zata kama matasan ƴan TikTok su guda biyu wato Ahmad Isa da kuma Maryam Musa wacce akafi sani da Maryam madogara dukkanninsu yan unguwar Ladanai a yankin Hotoron jihar Kano.
A yayin gurfanar dasu a gaban kotun Lauyan gwamnatin jihar Barista Garzali Maigari Bichi ya tuhume mutanen biyu da haɗa baki wajen aikata manyan laifuka baya ga wallafa saƙon da ya ci karo da tarbiyyar addini da kuma dokokin jihar ta Kano, laifukan da dukkaninsu suka amsa aikatawa.
Read also: Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar
A Karanta Wanna:Mun Fasara Littafin Sunayen Ma’aikatu Da Hausa, Don Saukakawa Abokan Aiki – Dan jarida Muhammad
Sanarwa da ta fito daga Jami’in Yaɗa Labarai na Hukumar tace fina-finai da Dabi’u ta jiha, Abdullahi Sani Sulaiman ta ce hukumar ba za tai kasa a gwiwa ba wajen gabatar da duk mai kuna kashi a gaban kotu




























