Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar

Kano
Kano

Zargin Almundahana: Kotu Ta Umarci Bankin UBA Ya Riƙe Kuɗin Kano Da Aka Karkatar

Daga Sunusi K/ Naisa

Babbar Kotun tarayya dake Abuja ta umarci Bankin UBA “United Bank of Africa” da ya rike kuɗin Jihar Kano da ake zargin “DG Protocol” na gwamnan Kano wato Abdullahi Rogo da karkatarwa da yawansu ya kai naira miliyan dubu da miliyan 100 Ɗaya.

Kotun ƙarƙashin Alƙali justis Emeka Nwite ta bada da umarnin ne bayan lauyan hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da aikata almundana wato ICPC ya gabatar da bukatar hakan.

Alkali ya yanke hukuncin cewa bukatar ta yi daidai kuma ya amince da ita.

Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya

Ya kuma bayar da umarnin a buga umarnin ƙwace kuɗaɗen a cikin wata jaridar kasar nan don baiwa duk wani mai sha’awa damar bayyana a gaban kotun da kuma nuna dalilin da ya sa bai kamata a miƙa kuɗaɗen ga Gwamnatin Tarayya ba har abada.

An ɗage shari’ar har zuwa ranar 21 ga Janairu, 2026, don bayar da rahoton bin ƙa’ida.

An shigar da ƙarar ne a ranar 3 ga Disamba kuma Z.S. Nass, Mataimakin Darakta a ICPC, ya shigar da ita a ranar 8 ga Disamba.

Duk Wanda Ya Tafi Jam’iyyar APC ya Tafi Shi Kaɗai, In ji Sanata Rufai Sani Hanga

Hukumar ICPC na neman umarnin wucin gadi na ƙwace kuɗin Naira 1,109,230,000 ga Gwamnatin Tarayya, kasancewar kuɗin da ake zargin an samo ne daga ayyukan da ba bisa ƙa’ida ba.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...