Connect with us

Hi, what are you looking for?

Siyasa

Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya

Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa
Hon. Hashim Sulaiman Dungurawa

Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya

Daga Wakilinmu

Shugabannin zartarwa na jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a mazabar Gargari Ward, da ke ƙaramar Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano, sun sanar da tsige Shugaban Jam’iyyar NNPP na Jihar Kano, Hashimu Dungurawa, daga jam’iyyar.

Matakin ya biyo bayan ƙudirin da mambobin zartarwa 27 na mazabar suka amince da shi, a yayin taron zartarwa na biyu da aka gudanar makonni biyu bayan sake zabensa.

Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban mazabar , Shuaibu Hassan, tare da Sakatarensa Yahaya Saidu Dungurawa.

Ƙungiyar RATTAWU Na Ta’aziyya Ga Gwamna Abba Yusuf Bisa Rashin Hazziƙan ‘Yan Majalisa Ungogo da KMC

A cewar ƙudirin, an tsige Hashimu Dungurawa ne bisa zargin haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyya, da tayar da rikice-rikicen cikin gida, da gazawar biyan kuɗaɗen jam’iyya, da kuma furta kalaman batanci ga Gwamnan Jihar Kano.

Shugabannin mazabar sun bayyana cewa irin wadannan ayyuka sun sabawa ƙa’idojin jam’iyya, kuma suna lalata martaba, hadin kai da cigaban NNPP a jihar.

Sun jaddada cewa an ɗauki matakin ne cikin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, domin tabbatar da da’a, zaman lafiya da haɗin kai a cikin jam’iyyar.

Haka kuma, sun ce an aika kwafin ƙudirin tsige shi zuwa ga shugabannin jam’iyyar a matakan Ƙaramar Hukuma, Jiha da kuma Ƙasa, domin ɗaukar matakan da suka dace.

Haka kuma, an sanar da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin bayar da umarnin da ya dace.

Shugabannin Gargari Ward sun ce wannan mataki zai zama izina ga duk wanda ke amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba, ko kuma yake ganin ya fi dokoki da ladabtarwar jam’iyya karfi.

Zancen Teburin Mai Shayi: Waye Kai Da Zaka Ce A Janye ‘Yan Sanda daga Nassarawa, Aminu Babba ya Kalubalanci Kwankwaso

Shugabannin sun sake jaddada biyayyarsu ga jagorancin NNPP na kasa karkashin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da cikakken goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, suna kuma tabbatar da kudirinsu na kare zaman lafiya, hadin kai da ci gaban jam’iyyar a dukkan matakai.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...