Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Daga Edita
Read also: Jam’iyyar NNPP ta Kori Shugabanta Na Kano, Hashimu Dungurawa daga Jam’iyya
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayyana goyon bayanta ga shirin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ficewa daga jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP), inda ta danganta hakan da rikice-rikicen shugabanci da kuma shari’o’in kotu da dama da ke addabar jam’iyyar, wanda ka iya barazana ga sahihancin mulkinsa.
Da yake zantawa da ’yan jarida a ranar Alhamis, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Lawan Hussaini Dala, ya ce ci gaba da kasancewa a jam’iyyar NNPP ya zama abin haɗari, ba ga gwamnan Abba kaɗai ba har ma ga sauran zaɓaɓɓun shugabanni a Jihar Kano.
Ya bayyana cewa a halin yanzu jam’iyyar na fama da rikicin shugabanci da kuma shari’o’i a kotu, wanda ya jefa shakku kan sahihancin tsarin jam’iyyar da kuma ingancin tsayawar ’yan takararta a zaɓuka masu zuwa.
“ Akwai hukuncin kotu da ya amince da wani ɓangare na NNPP,” in ji Hussaini. “Ba za mu iya ci gaba da zama a jam’iyyar ba mu sake fuskantar irin bala’in shari’a da ya faru a Jihar Zamfara.”
A cewarsa, waɗannan damuwa ne suka sa Majalisar ke goyon bayan kiran da ake yi ga Gwamna Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, su yi la’akari da barin NNPP zuwa wata jam’iyya da ta fi kwanciyar hankali a siyasa, ciki har da jam’iyyar APC.
Read also: Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa
Hussaini ya ce ’yan majalisar suna tuntuɓa da Yusuf da Kwankwaso domin cimma matsaya guda kan abin da ya kira “ficewa ta dabaru kuma a kan lokaci” daga jam’iyyar.
Ya yi gargaɗi cewa ci gaba da rikicin shugabanci da shari’o’in rarrabuwar kawuna a NNPP na iya kaiwa ga hukuncin kotu da zai soke ’yan takarar jam’iyyar ko da sun ci zaɓe.
A cewarsa, irin wannan yanayi na iya kaiwa ga tsige Yusuf da sauran masu riƙe da mukamai na NNPP ta hannun kotu, kamar yadda ya faru a Jihar Zamfara.
A zaɓen shekarar 2019, jam’iyyar APC ta lashe kusan dukkan kujerun zaɓe a Zamfara, ciki har da gwamna da kujerun majalisar jiha. Sai dai rikicin cikin gida ya hana gudanar da sahihan fidda gwani (primaries).
Kafin rantsarwa, Kotun Koli ta yanke hukuncin cewa APC ba ta da sahihan ’yan takara, ta ayyana kuri’un da aka kaɗa mata a matsayin ɓatattu, tare da umartar ayyana ’yan takarar da suka zo na gaba kuma suka cika sharuddan kundin tsarin mulki a matsayin masu nasara.
Wannan hukunci ya bai wa ɗan takarar PDP, Bello Matawalle, kujerar gwamna, yayin da jam’iyyar ta kuma samu kusan dukkan kujerun majalisa duk da ta sha kaye a akwatin zaɓe.
Gidauniyar Kashe Kwabo ta Gudanar da Aikin Idanu da Kaciya ga Ya’yan Marayu 602 Kyauta A Kano
Read also: Kishin Bunƙasar Kano Shi Yasa Gwamna Yusuf Ya Yi Sauyin Sheka – NNPP
A halin da ake ciki, tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya gargaɗi mambobin da suka fice ko ke shirin ficewa daga tafiyar, inda ya ce dole ne su yi hisabi kan goyon baya da ƙoƙarin da aka zuba musu kafin su bar tafiyar.
Platinum Post News



























