Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa
Daga Sunusi K/Naisa
Read also: Majalisar Dokokin Kano ta Amince da Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamnan
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta sanya ranar Litinin, 27 ga watan Afrilu, 2026 domin tantance Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan Kano, wanda Gwamna Alhaji Abba Yusuf ya gabatar da sunansa domin tantancewa.
Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Jibrin Ismaila Falgore ne ya bayyana hakan yayin zaman majalisar na wannan rana ta laraba.
Read also: Majalisar Dokokin Kano ta goyi bayan Gwamna Yusuf Ya fita Daga Jam’iyyar NNPP
Jibril Falgore ya karanta wasiƙar da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya turawa majalisar domin bukatar tantancewa tare da amince masa ya naɗa Murtala Sule Garo a matsayin Mataimakinsa.
Ga Wasu Labarun:
Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
An Sace Sarki da Ɗan Kasuwa da Mutane 13 a Alkaleri, In ji Galan Gwana
Idan za a tuna, tuni ta Gwamna Abba Kabir Yusuf ya miƙa sunan Murtala Sule Garo domin zama mataimakin gwamna, bayan murabus ɗin Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo a watan da ya gabata.
A bisa kundin tsarin mulkin Najeriya zarar majalisa ta aminta da kwarin wanda aka turamata domin tantacewa , toh zata mayarwa da da Gwamna domin ɗaukar mataki na gaba, wato shine tabbatar da shi a wanna kujerar tare da rantsar da shi don kama aiki.




























