Connect with us

Hi, what are you looking for?

Siyasa

Majalisar Dokokin Kano ta Amince da Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamnan

Murtala Garo
Murtala Garo

Majalisar Dokokin Kano ta Amince da Murtala Sule Garo a Matsayin Mataimakin Gwamnan

Daga Sunusi K/Naisa

Majalisar Dokokin jihar Kano ta amince da bukatar gwamna Abba Kabir Yusuf na neman naɗa Murtala Sule Garo a matsayin mataimakin gwamnan.

Majalisar Dokokin ta Kano dai ta Amince da Murtala ne bayan da kwamitin da ta naɗa ƙarƙashin jagoranci Mataimakin Shugaban Majalisar Hon. Muhammad Bello Butu-butu ya gabatar da rahotonsa.

Kwamitin tantancewa na Majalisar Dokokin Jihar Kano ya bayyana cewa ya yi cikakken nazari kan takardun karatun Murtala Garo, kwarewarsa a aiki da kuma tarihin rayuwarsa, bisa tsarin tantancewar da majalisar ke bi.

Bayan tattaunawa kan rahoton kwamitin, ‘yan majalisar sun amince baki ɗaya da rahoton da aka gabatar, inda suka tabbatar da Garo a matsayin wanda ya cancanta kuma ya dace ya zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano.

Daga nan ne Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, ya sanar da amincewar majalisar, lamarin da ya baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf dama domin rantsar da Garo a matsayin sabon mataimakin gwamna.

Ga Wasu Labarun:

Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa

Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar Abduljabar, ta umurci a hanzarta sauraron shari’ar a Babbar Kotun Kano

Idan za’a tuna a ranar Talata ta makon da ya gabata ne gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya miƙa wa majalisar sunan Murtala Sule Garo domin a tantance shi a kuma amince masa ya naɗa shi a kujerar mataimakin gwamna Kano .

Hakan ya biyu bayan murabus na tsohon mataimakin gwamnan na Kano Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo ya ajiye mukaminsa sskamakon tuhumar siyasa wacce ta haifar da canjin shekar Gwamna Abba zuwa Jam’iyyar APC, a inda mataimakin sa ya bijirewa bin Gwamna zuwa APC.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...