Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

“Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba Kabir Yusuf

“Ku Bar Ofisoshi Ko Ku Fuskanci Hukunci,” Gwamnatin Kano Ta Gargadi Ma’aikatan Da Suka Kai Ritaya

Daga Sunusi K/Naisa

Gwamnatin Jihar Kano ta umarci ma’aikatan gwamnati da suka kai shekarun yin ritaya ko suka cika wa’adin aikin da doka ta tanada da su gaggauta barin ofisoshinsu tare da miƙa takardun gwamnati da kadarorin gwamnati da ayyukansu ga waɗanda ke ƙarƙashin su.

Umarnin na ƙunshe ne a cikin Circular mai lamba 10/2026, ɗauke da kwanan wata 6 ga Oktoba, 2026, wadda Sakataren Din-din-din mai kuɗa da Ma’aikata, (Establishment), Abba A. Danguguwa, ya sanya wa hannu a madadin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar.

Takardar mai lamba HCS/GEN/3/T.1 ta ce gwamnatin ta lura cewa wasu ma’aikatan gwamnati na ci gaba da zama a ofisoshi tare da gudanar da ayyukan hukuma bayan sun kai lokacin ritaya ko sun kammala wa’adin aikin da doka ta tanada.

Farfesa Pantami Ya Samu Nasara A Sabon Zaɓen Ɗan Takarar Gwamnan Gombe A PDP

Gwamnatin ta bayyana cewa irin wannan ɗabi’a ta saɓa wa tsarin da aka daɗe ana bi na tabbatar da miƙa ragamar aiki cikin tsari da mutunci da kima ga ma’aikatan da suka yi ritaya.

Ta gargadi ma’aikatan da abin ya shafa cewa ci gaba da zama a ofis bayan cikar lokacin ritaya ya saɓa wa dokokin aikin gwamnati na Jihar Kano da sauran ƙa’idojin da suka dace.

Gwamnatin ta kuma umarci Sakatarorin Din-din-din, shugabannin hukumomi da daraktocin da ke kula da harkokin ma’aikata da su tabbatar da bin umarnin nan take. Ta gargadi jami’an da suka taimaka, suka goyi baya ko suka ƙyale ma’aikatan da suka yi ritaya su ci gaba da aiki cewa za su fuskanci matakin ladabtarwa.

Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano

Matakin na gwamnatin Kano na da nufin tabbatar da bin dokokin ritaya tare da sauƙaƙa miƙa ragamar ayyuka cikin tsari ga sabbin jami’an da za su ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...