Hukumar Shari’a ta Yi Wa Wasu Alƙalai da Ma’aikata Ritayar dole A Jihar Kano
Daga Sunusi K/Naisa
Hukumar kula da ma’aikatan Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta tilasta yin ritayar dole ga wani alkalin kotun shari’a da kuma wani babban jami’in kotu bayan samun su da laifukan cin hanci da kuma gabatar da takardun shaidar karatu na bogi.
Read also: Hukumar Tace Fina-Finai da Ɗab’i ta Jiha Ta Ce Har Yanzu Sana’ar Downloading Halattacciya Ce A Kano
Mai magana da yawun ma’aikatar shari’ar Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya ce an ɗauki matakin ne a taron hukumar na 90 bayan nazarin rahotannin Kwamitin Karɓar Korafe-korafen Jama’a kan zarge-zargen rashin ɗa’a da suka shafi alkalai da ma’aikatan kotu.
Baba jini ya ce an tilasta wa Alƙali Aliyu Yahaya Muhammad na Kotun Shari’ar Babeji ritaya bayan an same shi da laifin karɓar cin hancin kuɗi Naira 250,000, tare da umurtarsa da ya mayar da kuɗin. Haka kuma, an dakatar da Magatakardar kotun, Ibrahim Ahmad Ibrahim, na tsawon watanni huɗu ba tare da albashi ba saboda amsa karɓar wani ɓangare na kuɗin.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Hakazalika, an tilasta Mukaddashin daraktan hulɗa da Jama’a na kotun Ɗaukaka Ƙara ta Shari’a, Muzambilu Ado, ritaya bayan an gano ya yi amfani da takardun bogi wajen samun aiki.
JSC ta kuma rage wa Alƙali Usman Haruna Usman na Kotun Shari’a ta Goron Dutse matsayi da daraja guda saboda sakaci da ya janyo asarar kuɗin masu ƙara, tare da tabbatar da dakatarwar shekara guda da aka yi masa a baya.
An Nemi a Gyara Auran Matasa Da Sukai Aure Akan Sadaki ₦3000, A Maimakon Dauri
Hukumar ta yi barazanar ci gaba da ɗaukar tsauraran matakai kan duk wani jami’in shari’a da aka samu da laifin cin hanci, rashawa ko amfani da mukami ba daidai ba.




























