Connect with us

Hi, what are you looking for?

Afirka

Kwamitin Muhuyi a Kano Ya Kama Kwayoyin Pregabalin da Ake Zargin Miyagun Kwayoyi Ne Na Miliyan 3.18, Kasa da Sa’o’i 24 Bayan Ƙaddamar da Rundunar Rapid Response Squad

An kama kwayoyin Pregabalin na miliyan 3.18 A Kano
An kama kwayoyin Pregabalin na miliyan 3.18 A Kano

Kwamitin Muhuyi a Kano Ya Kama Kwayoyin Pregabalin da Ake Zargin Miyagun Kwayoyi Ne Na Miliyan 3.18, Kasa da Sa’o’i 24 Bayan Ƙaddamar da Rundunar Rapid Response Squad

Rundunar Haɗin Gwiwa ta Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Jihar Kano ta ƙwace kimanin kwayoyi miliyan 3.18 da ake zargin Pregabalin ne a yankin Sabon Gari da ke cikin birnin Kano, ƙasa da sa’o’i 24 bayan Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da rundunar gaggawa ta Rapid Response Squad a hukumance.
Bisa ɗaukar mataki cikin gaggawa bisa bayanan sirrin da aka samu, jami’an rundunar sun gano tare da gudanar da bincike a wani gidan zama mai lamba 13 da ke Apple Avenue, Normansland, Sabon Gari, a Ƙaramar Hukumar Fagge, wanda ake zargin ana amfani da shi wajen gudanar da haramtattun ayyuka.
A yayin samamen, jami’an rundunar sun gano tare da ƙwace kimanin kwayoyin Pregabalin guda 3,180,000 da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne, tare da kama wani mutum mai shekaru 34 da haihuwa mai suna Gregory Ogbuji.
Ana zargin wanda aka kama yana da alaƙa da kamfanin SEEMARK PHARMA LTD, mai lambar rajista ta 2012546. An gurfanar da shi bisa sashe na 249 na kundin dokokin Penal Code. Sai dai wani mutum da ake zargin yana da hannu a lamarin har yanzu yana tsere, kuma hukumomi na neman sa.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...