BASHI NA DAF DA DURKUSAR DA NAJERIYA
Najeriya na fuskantar wani mawuyacin hali da ke barazana ga makomarta, kuma Ofishin Kula da Basussukan Ƙasa (Debt Management Office – DMO) ya bayyana hakan karara ba tare da ɓoye komai ba.
Ya zuwa shekarar 2030, ana hasashen cewa biyan kuɗin hidimar bashi zai iya cinye kashi 71.7 cikin 100 na kuɗaɗen shiga na Gwamnatin Tarayya. A wani yanayi mafi muni da adadin zai iya kaiwa har kashi 97.3 cikin 100. Wannan ba hasashe ba ne da ya kamata a ɗuke Kai daga gareshi ba, ba tare da anyi duba na tsanaki da kuma nazari mai zurfi a kansa ba. Haka kuma babbar barazana ce ga ƙasa baki ɗaya da ke buƙatar ɗaukar matakin gaggawa.
Ƙasar da kusan duk kuɗin da take samu ke tafiya wajen biyan basussukan da ta ci a baya, ba za ta samu sauran kuɗaɗen da za ta yi amfani da su wajen gina kanta ba. Ba za ta iya samar da isassun kuɗaɗen gudanar da makarantu da asibitoci da gina hanyoyi da bada ingantaccen tsaro ko samar da ayyukan yi ba. Abin da za ta iya yi kawai shi ne ci gaba da tafiyar hawainiya zuwa koma-baya.
Sai dai duk da haka, gwamnati ta mayar da karɓar bashi a matsayin hanya mafi sauƙi a duk shekara, alhali kuwa ita ce hanya mafi muni da ke jefa ’yan ƙasa cikin wahala. Daga bashin Naira tiriliyan 27.40 a shekarar 2019 zuwa Naira tiriliyan 166.788 a watan Yunin 2026, idan akai duba da kyau, bashin ƙasar ya ninka har sau shida. Amma rayuwar talakawan Najeriya ba ta inganta ba, ballantana tai daidai da wannan ƙarin bashi da aka ci ba.
Jaridar The Stentor news na ganin cewa lokacin bayar da uzuri ya huce.
Dole ne gwamnati ta ɗauki matakai uku cikin gaggawa domin samun mufita ga Wanna mumunan halin taɓarɓarewar arzikin ƙasa da ake fuskanta Najeriya:
A DAINA KARƁAR BASHI DOMIN BIYAN KUƊAƊEN AMFANI NA YAU DA KULLUM
Karɓar bashi domin biyan albashi, tallafi da sauran kuɗaɗen gudanar da ayyukan yau da kullum tamkar cin abincin gobe ne a yau. Sabbin basussuka ya kamata a karkata su kawai zuwa ayyukan raya ƙasa da za su iya samar da kuɗaɗen da za su biya kansu, kamar samar da wutar lantarki da sufuri da noma da kuma manyan ayyukan more rayuwa da za su samar da arziki da ayyukan yi. Duk wani abu da ya saɓa da wannan, almubazzaranci ne da dukiyar ƙasa.
A ƘARA KUƊAƊEN SHIGA, BA TARE DA ƊORA WA ’YAN ƘASA WANI ƘARIN HARAJI BA
Faɗaɗa hanyoyin tattara haraji ba yana nufin gallaza wa ƙananan ’yan kasuwa ba ne, yayin da manyan masu kauce wa biyan haraji ke ci gaba da samun ’yanci, wanda ya zama dole a canja hakan.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
Abin da hakan ke nufi shi ne toshe hanyoyin zubar da kuɗaɗen gwamnati da tilasta wa kamfanonin gwamnati da sauran hukumomin da ke da alhakin biyan kuɗi su biya abin da ya rataya a wuyansu, sayar da kadarorin gwamnati da ba a amfani da su, tare da tabbatar da cewa tsarin haraji ya kasance na adalci, gaskiya da kuma amfani ga ƙasa.
’Yan Najeriya za su fi yarda su biya haraji idan sun ga amfanin kuɗaɗen harajin da suke biya.
A RAGE KUƊAƊEN GUDANAR DA GWAMNATI
Ba daidai ba ne Najeriya ta riƙa kira ga ’yan ƙasa da su yi haƙuri da sadaukarwa, alhali gwamnati na rayuwa cikin almubazzaranci da jin daɗin na wuce kima ga uwa-uba handama da babakere da dukiyar al’umma.
Dole ne a kawo ƙarshen maimaita ayyukan hukumomi da almubazzaranci da ƙara farashin kwangiloli fiye da kima da kuma tsadar gudanar da gwamnati sakamakon yawan kashe kuɗaɗen da ba su zama dole ba mutuƙar ana son farfadowar ƙasar nan.
Dole ne a fara bin tsarin kula da kuɗaɗen gwamnati yadda ya kamata daga manyan shugabanni, ba wai a ƙara matsa wa ƙananan ’yan kasuwa a kasuwanni ba.
DMO ta yi gargaɗi. Alkaluma sun bayyana gaskiya. Yanzu zaɓin yana hannun ’yan siyasa da shugabannin ƙasa.
Najeriya na da zaɓi biyu: ko dai ta ɗauki tsauraran matakai a yau domin dawo da ƙarfin tattalin arzikinta da damar gudanar da ayyukan ci gaba, ko kuma ta ci gaba da karɓar bashi, biyan basussuka da kuma jinginar da makomar ‘ya’yenta wanda ba su ne da alhakin karɓar waɗannan basussukan ba.
Ba za a iya tafiyar da ƙasa mai yawan al’umma sama da miliyan 230 da Naira 28 kacal daga cikin kowace Naira 100 da take samu ba.
Dole ne mu koyi rayuwa gwargwadon abin da muke da shi, mu karɓi bashi kawai domin bunƙasa tattalin arziki, sannan mu kashe kuɗaɗen ƙasa domin amfanin al’umma, ba domin biyan masu bashi ba.
Kada a yi amfani da makomar ƙasa wajen biyan kuɗin kurakuran da aka tafka a baya ba.




























