Sankarar Mama: Cibiyar Magungunan Gargajiya ta Karkare Ta Nuna Damuwa Kan Karuwar Cutar Ga ‘Yanmata a Kano
Daga Sunusi K/Naisa
Cibiyar Magungunan Gargajiya ta Karkare ta bayyana damuwa ainun kan yadda ake samun ƙaruwa mai yawa na masu fama da cutar dajin mama (Breast Cancer) a tsakanin matasa mata a Jihar Kano.
Read also: Gwamnatin Kano Na Faɗakar Wa Kan Cutar Lassa, Ta Ja Hankali Game Da Haɗarin Yaɗuwar Cutar
Shugaban cibiyar, TMP Adamu Yusuf Kofar Na’isa Kakan, ne ya bayyana hakan yayin gangamin wayar da kan jama’a kan cutar kansa na shekara-shekara da cibiyar ta gudanar a ranar Lahadi a rufafan ɗakin taro na Filin Wasanni da ke Kofar Mata, Kano.
A cewarsa, cibiyar ta fuskanci ƙaruwa mai matuƙar yawa na marasa lafiya masu fama da cutar dajin mama da ke neman magani cikin shekaru biyu da suka gabata.
Ya bayyana cewa yayin da cibiyar ta karɓi marasa lafiya 180 masu fama da cutar kansa a cikin shekaru biyu da suka gabata, adadin ya ƙaru zuwa mutum 876 daga shekarar 2024 zuwa yanzu, lamarin da ya bayyana a matsayin abin matuƙar tayar da hankali.
Ya ƙara da cewa daga cikin adadin marasa lafiyar da cibiyar ta karɓa, mutum 182 sun samu cikakkiyar lafiya bayan jinya, inda ya bayyana cewa mafi yawan waɗanda cutar ta shafa matasa mata ne masu shekaru tsakanin 10 zuwa 15.

Ya buƙaci mata su guji amfani da duk wani nau’in sinadari ko magani da ka iya jefa lafiyarsu cikin haɗari tare da ƙara musu yiwuwar kamuwa da cutar dajin mama da sauran cututtuka masu alaƙa da ita. Ya kuma shawarce su da su nemi shawarar ƙwararrun ma’aikatan lafiya kafin amfani da duk wani magani ko sinadari.
Masanin magungunan gargajiyar ya kuma yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta umurci Ma’aikatar Lafiya ta jihar da ta gudanar da cikakken bincike kan yadda cutar kansa, musamman dajin mama, ke ƙaruwa a jihar tare da gano hanyoyin magance matsalar cikin hanzari.

Haka kuma, ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya amince da haɗa ƙwararrun masu magungunan gargajiya cikin tsarin samar da ingantaccen kiwon lafiya a faɗin jihar.
Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf
Da yake jawabi a wajen taron, Attajiri, Alhaji Salisu Linder, ya yaba wa Cibiyar Magungunan Gargajiya ta Karkare bisa jajircewarta wajen wayar da kan jama’a da kuma kula da masu fama da cutar kansa, musamman mata.
Ya kuma yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya taimaka wa cibiyar da ginin gurin na dindindin ma yalwaci, yana mai cewa ginin da take amfani da shi a halin yanzu ba ya iya ɗaukar yawan marasa lafiyar da ke neman magani.
Alhaji Salisu ya kuma yi alƙawarin bayar da gudummawar Naira miliyan 10 domin tallafawa mata 500 da ke fama da cutar domin su rage raɗaɗi.
Read also: Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf
Gangamin wayar da kan jama’ar na bana karo na uku me taken: ‘Zama Lafiya Yafi Zama…’ ya samu saƙonnin fatan alheri daga manyan baƙi da dama, ciki har da malamin jami’a kuma Shugaban Gidauniyar Safinatul Khair, Farfesa Ibrahim Mai Bushira da Hakimin Gwale, Turakin Kano, Alhaji Mahmoud Ado Bayero, wanda Alhaji Aminu Tijjani Sanusi (Wakilin Fuskar Yamma) ya wakilta da wakilin Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano da kuma sauran ƙwararrun ma’aikatan lafiya.
Taron ya samu halartar daruruwan mahalarta, musamman mata, ciki har da waɗanda suka warke daga cutar dajin mama da kuma waɗanda ke ci gaba da karɓar magani, lamarin da ya nuna irin damuwar da al’umma ke nunawa game da yaɗuwar cutar a Jihar Kano.




























