Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf

Shugaban Cibiyar Karkare Herbal TMP Adamu Yusuf
Shugaban Cibiyar Karkare Herbal TMP Adamu Yusuf

Yaɗuwar Sankarar Mama: Mata 500 Sun Kamu a Kwana 210 – TMP. Adamu Yusuf

Daga Sunusi K/Na’isa

Shugaban Ƙungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Gwale, TMP. Adamu Yusuf, ya bayyana damuwa kan yawaitar masu fama da cutar sankarar mama a jihar Kano.

A cewarsa, Cibiyar Maganin Gargajiya ta Karkare ta samu fiye da mata 500 da aka gano suna ɗauke da cutar sankarar mama cikin watanni bakwai kacal — abin da ya bayyana a matsayin abin damuwa matuƙa.

Malam Adamu Yusuf ya bayyana haka ne a yayin gangamin wayar da kan jama’a kan cutar sankarar mama wanda cibiyar ta saba yi a kowace shekara, da aka gudanar a ranar Asabar a dakin taro na Kofar Nasarawa Cooperative Society.

Kotu Ta Daure Wani Mutum Wata 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano

Ya ce babban burin taro shi ne ilimantar da mata yadda za su gane alamomin cutar tun da wuri tare da karfafa musu guiwar tuntubar masana lafiya cikin gaggawa yayin da suka ankara da samun canjin wani baƙon al’amari a jikinsu.

IMG 20250802 113250

Alhaji Adamu Kakan, ya ce tun kusan shekaru 30 da suka wuce, cutar sankara mama baƙuwa ce a nahiyar Afirka ko ma ba a santa ba, bale kuma ƙasar Najeriya. Bincike ya tabbatar da ƙasashen yamma su aka fi sani da da cutar. Amma yanzu, ya ce cutar ta shiga ƙasashe daban-daban kuma babu rukunin matan da cutar ta bari ciki har da jarirai.

Ya yi kira ga gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai don dakile yaɗuwar cutar sankarar mama a cikin al’umma cikin hanzari.

Adamu ya ƙara da cewa Cibiyar Karkare ta maganin gargajiya ta yi jinyar mutane sama da 10,900 masu Larural Karkare tun daga watan Janairun bara zuwa wanna watan.
Ya bayyana talauci da jahilci da halin ko-in-kula su ne manyan abubuwan da ke haddasa yaɗuwar cutar sankara mama, sannan ya roƙi gwamnati da ta tallafa wa masu fama da cutar da kuma cibiyoyin maganin gargajiya a jihar Kano don samun nasarar kawar da ita.

A nata jawabin, Mai ba Gwamnan Kano shawara kan harkokin mata, Hajiya Rabi Adamu Hotoro, ta tabbatar da ƙudurin gwamnatin jihar na ci gaba da goyon bayan cibiyoyin masu maganin gargajiya. Haka kuma ta yaba da rawar da suke takawa wajen tabbatar da lafiyar jama’a, sannan ta ce za ta isar da sakon taron zuwa ga Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf domin ɗaukar matakin da ya kamata.

Da yake jawabi, Malam Nura Salisu Adamu (Salihannur) ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin likitoci da masu maganin gargajiya a jihar Kano. Ya nunar da rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) cewa kashi 75% na al’ummar duniya suna amfani da maganin gargajiya – musamman a ƙasashen da suka ci gaba inda gwamnati ke tallafa wa harkar, sai ya bukaci gwamnatocin ƙasar nan da su farka domin aiki da masu maganin gargajiya ko a samu raguwar yaɗuwar cuttuka.

Ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda shugabannin Najeriya ke nuna halin ko-in-kula game da harkar maganin gargajiya, inda ya bukaci a ƙara haɗin gwiwa da duk masu ruwa da tsaki don magance ko kawar da cutar gaba ɗaya.

Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo

Taron ya samu halartar masana daga jami’o’i da kuma manyan masu maganin gargajiya kamar su Dr. Aisha Umar Adamu daga Jami’ar BUK, Farfesa Maryam Mansir Yola da Farafesa Yahaya Imani da kuma Sarkin Hausawa na ƙasar Binin, Alh. Aliyu Kabir da Dr. Arab Dan Sokoto, wanda shine shugaban Ƙungiyar Masu Maganin Gargajiya ta Jihar Kano.

Jigon taken taron na shekara 2025 shine: “Ku Tashi Ku Farka Mata Daga Kamuwar Sankarar Mama.”

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...