Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Wasu Ma’aikatun Gwamnati Zasu Sami Sabbin Shugabanni A Kano
Wani tsohon Shugaban Kotun Kula da Ɗa’ar Ma’aikata a tarayyar Najeriya Barista Mainasara Umar Kogo ya ce bai taɓa cin haram ko karɓar rashawa a tsahon shekaru 35 da ya yi yana aikin gwamnati a tarayyar Najeriya ba.
Mainasara Kogo ya furta haka a wata hira da ya yi da kafa yaɗa labarai ta Faransa wato rFi Hausa.
Shugaban wanda haifaffen Najeriya ne wanda ya riƙe muƙamai daban-daban har ya kai matakin Babban mai Shari’a a Kotun kula da Da’ar Ma’aikata ta ƙasa, ya tabbatar da cewa shi bai karɓar Haram kuma bai cin haram.
Read also: Shugaba Donald Trump Ya Soke Visa Dubu 80 Ta ‘Yan Najeriya Da Wasu Kasashen Waje
” Kai hatta motar office ɗina ma, ƙarfe 4 na yamma na yi nake ajeye ta in hau motar haya zuwa gida saboda kasancewar lokacin da akai umarni a tashi daga aiki ya yi, tunda nake ban taɓa ci haram ba” ina ji Barista Kogo.
Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
Bilhasali ma, ya ce kwamitin ya kafa ɗinguringun da zai riƙa bin abin da yake aikatawa tare bin diddigi ko bincikar sa a matsayin Shugaban Kotun Kula da Ɗa’ar Ma’aikata a Najeriya a lokacin da aka naɗa shi. Haka kuma ya umarci kwamitin ya riƙa tura rahoto ga Shugaban Alkalai Alkalai na Najeriya da shugaban hukumar ‘yan sanda na ƙasa da EFCC da ICPC da DSS da Ministan Shari’a da dukkanin hukumar da ta kamata, batare da nuna masa kwafi na rahoton ba.
Ya ce ya yi hakan ne domin a fara yi masa hisabi tun a duniya kafin ya je lahira. Haka kuma ya ce ya bukaci duk waɗanda ke aiki a karkashin sa da su kiyaye tare da ruke gaskiya da amana.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Yunwa: Sakamakon Rashin Abinci Mai Gina Jiki Yara Sama da 650 Sun Halaka a Katsina -MSF
” Ni ban san daɗin gado ko katifa ba a ƙasa nake kwana tsawon shekaru 35 dana shafe ina aikin gwamnati, yanzu har nayi ritaya ko mota ban da ita”. Kamar yadda Mainasara ya faɗa. (rFi Hausa).




























