Yunwa: Sakamakon Rashin Abinci Mai Gina Jiki Yara Sama da 650 Sun Halaka a Katsina -MSF
Daga Sani Aminu
Wata ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa (MSF) wacce ta fara aiki a Katsina tun shekarar 2021, ta ce ta samu ƙaruwar yara masu fama da yunwa sanadiyyar rashin abinci mai gina jiki da aka isar da su zuwa cibiyoyin kula da marasa lafiya da ƙungiyar ke da su a yankin.
Read also: Rashin Tallafin Kuɗi Nijeriya Tai Asarar Gangaran a Fanin Kwamfuta, Prof. Roko
Tsakanin Janairu da watan Yuni 2025, ƙungiyar MSF ta ce ta yi jinyar kusan yara 70,000 da ke fama da tamowa a jihar Katsina, ciki har da kusan 10,000 da ke bukatar kulawa da ta dace daga likitoci kamar yadda RFI Hausa suka ruwaito.
Read also: Ebola Ka Iya Hadasa Ɗage Zaɓen 2027 A Najeriya
“A wannan shekarar ta 2025 a cewar ƙungiyar , yara 652 suka mutu saboda rashin samun kulawa akan lokaci,” in ji Ahmed Aldikhari, mai magana da suna ƙungiyar ta MSF a Najeriya, kamar yada sanarwa ta tabbatar a ranar Juma’a 25 ga watan July 2025.
ƙungiyar ta ce ƴaran da iyaye sun fuskanci tarin mataloli ne sakamakon raguwar tallafin da ake samu daga ƙasashen duniya, inda manyan ƙasashe masu bayar da tallafi da suka haɗa da Amurka da Birtania da kuma Tarayyar Turai suka rage kuɗaɗen da suke bayarwa.




























