Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet

Kano pension
Kano pension

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet

Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na biyan kuɗaɗen giratuti (gratuity) da sauran haƙƙoƙin ma’aikatan gwamnati da suka rasu ko sukai ritaya daga aiki, inda za a riƙa biyan kuɗaɗen a duk wata domin tabbatar da biyan haƙƙin tsofaffin ma’aikatan gwamnati da iyalan waɗanda suka rasu a kan kari.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan yayin bikin rabon kashi na bakwai na kuɗaɗen giratuti da haƙoƙin waɗanda suka rasuwa, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin jihar Kano, a ranar Talata.

Ya bayyana cewa sabon tsarin zai maye gurbin tsohon tsarin biyan kuɗaɗen duk bayan watanni uku ko kuma ba bisa ƙa’ida ta lokaci ba, inda ya tabbatar wa waɗanda abin ya shafa cewa za a ci gaba da biyan kuɗaɗen a kowane wata har sai an biya dukkan kuɗaɗen da ake bin gwamnati.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta kammala mayar da tsarin biyan fansho na kowane wata zuwa tsarin kwamfuta (automation), tare da kammala ɗaukar bayanan sirri na masu karɓar fansho ta hanyar na’urar tantance halitta (biometric), a wani yunƙuri na tabbatar da gaskiya da riƙon amana da Kyautata gudanar da harkokin fansho.

Ya ƙara da cewa an kuma samar da tsarin tantance bayanan masu karɓar fansho lokaci zuwa lokaci, domin inganta wa da adana bayanansu da kuma daƙile duk wani nau’in rashin bin ƙa’ida.

A cewarsa, sabon tsarin tantance bayanan ta hanyar fasahar zamani zai bai wa masu karɓar fansho da ke zaune a cikin Najeriya da kuma ƙasashen waje damar tantance matsayinsu daga duk inda suke, ba tare da sun sha wahalar tahowa Kano ko kashe kuɗaɗe ba.

Saboda haka, Gwamna Yusuf ya buƙaci masu karɓar fansho da su sauke manhajar Kano State Pension Fund Trustees Pensioner Verification Application daga shagon manhajojin Google Play Store, domin kammala tantance bayanansu cikin sauƙi.

Gwamnan ya yabawa Hukumar Amintattun Asusun Fansho ta Jihar Kano (Kano State Pension Fund Trustees), Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jiha, Ma’aikatar Kuɗi da Ƙungiyar Masu Karɓar Fansho ta Najeriya (Nigeria Union of Pensioners), ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Comrade Godwin Abumisi, bisa gudunmawar da suka bayar wajen samun nasarar aiwatar da waɗannan sauye-sauye.

Ya kuma umarci jami’an gwamnati da abin ya shafa da su tabbatar da gaskiya da ƙwazo da amana wajen aiwatar da sabon tsarin biyan kuɗaɗen a kowane wata.

Gwamna Yusuf ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta biyan dukkan basussukan fansho da ake bi, kafin watan Afrilun shekarar 2027.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Lafiya

Daga Sunusi K/Naisa Hukumar kula da Manyan Asibitocin Jihar Kano ta magantu dangane da Ma’aikatan wucin-gadi da ta dakatar da aikinsu a Asibitocin gwamnati.Read...