Connect with us

Hi, what are you looking for?

Kotu

Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami

Prof Isa Ali Pantami
Prof Isa Ali Pantami

Kotun Tarayya a Gombe Ta Soke Zaben da Aka Yiwa Farfesa Isa Ali Pantami

Daga Wakilin mu

Babbar Kotun Tarayya dake Gombe ta soke zaɓen da aka gudanar wanda ya bawa Farfesa Isa Ali Pantami tikitin zama ɗan takara Gwamna ɗaya tilo a jami’ar PDP a jihar.

Haka kuma kotun ta umarci Jam’iyyar ta PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani domin tantance ɗan takararta na gwamnan Jihar Gombe.

Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta bayar da umarnin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar tsayar da Farfesa Isa Ali Pantami a matsayin ɗan takarar jam’iyyar ta PDP.

Kotun Ɗaukaka Ƙara ta kori ƙarar Abduljabar, ta umurci a hanzarta sauraron shari’ar a Babbar Kotun Kano

Garry ya ƙalubalanci tsayar da Pantami bayan PDP ta sanar da shi a matsayin ɗan takara ɗaya tilo a ranar 26 ga Yuni 2026, yana mai cewa ba a gudanar da zaɓen fidda gwani ba a bi ƙa’idojin da suka dace ba.

Pantami ya koma PDP ne bayan APC ta hana shi tikiti tsayawa takara tare da bawa Jamilu Gwamna damar a matsayin ɗan takararta na yarjejeniya.

Don haka kotun ta umarci PDP da ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani bisa ƙa’idojin jam’iyyar da kuma tanade-tanaden dokokin zaɓe.

Babbar Kotun Tarayya Abuja ta yanke hukunci ga wanda ya kitsa munanan hare-hare a Kano

A baya, Pantami ya samu tikitin PDP ne ta hanyar amincewar ɗaukacin ‘ya’yen jami’ar a yayin zaɓen fidda gwani da jam’iyyar ta gudanar a watan Mayu na wannan shekara.

1 Comment

1 Comment

  1. Pingback: Farfesa Pantami Ya Samu Nasara A Sabon Zaɓen Ɗan Takarar Gwamnan Gombe A PDP - The StentorNews Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...