Kotu Ta Daure Wani Mutum Shekaru 3 A Gidan Gyaran Hali Sakamakon Kona Taya A Kano
Daga Sunusi Ka/Na’isa
Read also: Dambarwar Sarautar Kano: Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukuncin Matsayar Huruminta
Wata kotun majistare mai lamba 2 a No-man’s-land da ke Sabon Garish Kano ta yanke wa Ibrahim Abubakar dan unguwar Tukuntawa hukuncin daurin watanni uku ko kuma biyan tara bisa samunsa da laifin kona tayoyin mota a bainar jama’a.
Da yake jagorantar shari’ar, Alkalin Kotun Mai shari’a Auwalu Yusuf ya cease kotu ta samu Abubakar da laifin keta dokokin muhalli da lafiyar jama’a, inda ya gargade shi da kada ya sake yin irin wannan abu saboda illar da suke da shi ga lafiyar dan Adam.
Read also: Kotu a Kano ta Daure ‘yan tiktok Shekara Guda Bisa Laifin Wallafa Bidiyon Batsa
Ban taɓa cin haram ba a shekaru 35 a aikin Gwamnati a Najeriya, in ji Barista Mainasara Kogo
Ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi ta jihar Kano, wacce Barista Bahijjah H. Aliyu ta wakilta ce ta shigar da karar. Jami’an ‘yan sanda masu sintiri ne suka cafke Abubakar a unguwar Tukuntawa Gidan Radio bayan da mazauna yankin suka kai rahotonsa saboda sakin hayaki mai guba ta hanyar kona tayoyi.
Bayan korafin, Daraktan kula da kare gurbatar muhalli na ma’aikatar, Ibrahim Nasir, ya jagoranci binciken in da daga bisani aka shigar da karar. An gabatar wa kotun da kwakkwarar shaida da ke nuna illar lafiyar da lamarin ke tattare da shi.
Read also: Kotu ta Umarci Masu Barkwanci Na TikTok A Kano Dasu Yi Aure Bayan Yaɗa Bidiyon “Futsara”
Belin Dan Safarar Kwaya: Gwamna Abba Ya Umurci A Gaggauta Bincikar Zargin Hannun Kwamishinan Sufuri
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka bawa The Stentor News Online, Daraktan wayar da kan jama’a, Murtala Shehu Umar, ya ce Ma’aikatar ta gamsu da hukuncin kotun, ya kuma nanata kudurin ma’aikatar na kare lafiyar jama’a da muhalli. Ya bukaci mazauna yankin da su guji ayyukan da ke kawo illa ga muhalli




























