Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Daga Abdullahi Alhassan, Kaduna
Read also: JAMB ta Dakatar Da Karatun Digirin Haɗaka Tsakanin Jam’i’o’i da Kwalejojin Ilimi A Najeriya
Wani Dattijo me yin sharhi kan al’amuran yau da kullum, (National president Arewa united consultative forum), Alhaji Ado Shu’lbu Dansudu, yayi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya ba Babban Bankin Ƙasar nan umurni don chenza takardar Naira, inda ya baiyana cewa yin hakan zai kawo ƙarshen riƙe kuɗi da yan ta’adda ke yi a ƙasar nan.
Ado Dansudu ya yi wan nan kira ne ya yin zan tawa da manema labarai, ya ƙara da cewa laile gaggauta chanza kalar kuɗin da Babban Bankin Najeriya zai yi zai kawo ƙarshen riƙe kuɗaɗen dake hannun yan ta’adda hakan kuma zai ragewa musu karfi. Domin sun karbi bilyoyin nairori a hannun yan Najeriya. Kuma zunzurutun kuɗaɗe wanda ko bankuna basa amfana haka ma ‘yan kasuwa. Don haka chanja kuɗin ne kawai zai koma dasu baya kuma susan gwamnati, gwamnati ce.
Shugaban Kungiyar yan Arewa Grassroots movement for Tinubu a Legas ya Kuma kara dace wa a shekarar 1983 Gwamnati Buhari ta chanja kalar naira, wai saboda ‘yan siyasa sun saci kuɗi ‘cash’ sun ɓoye a gidajen su.
Sannan a 2023 zuwa 2024 Gwamnati Buhari ta chanja kuɗi wai saboda a hana siyan kuri’a. Dan haka muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta chanja kalar kuɗin Najeriya watau naira. sannan asa jami’an DSS da EFCC a kowanne Banki domin damƙe marasa gaskiya.
Read also: Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya
Ga Wasu Labaran:
An Sace Sarki da Ɗan Kasuwa da Mutane 13 a Alkaleri, In ji Galan Gwana
Shugaban ‘Yan Bindiga Bello Turji Na yunƙurin Miƙa Wuya Bayan Mutuwar Yelo Danbokolo
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Haka kuma zasu sanya ido wajan masu kawo cash bankuna domin a chanja musu, san nan asa Hukumar leken asiri ta Ƙasar nan wato NIA. NFIU, da Costom, da hukumar shiga da fice wato (Immigration), a kan iyakokin ƙasar nan domin su sa ido ga masu chanja Naira zuwa wasu kudaden ƙasashen waje.
Ya kara dacewar “Wannan zai taimaka gaya wajan shawo kan rashin tsaron da muke fama dashi. Idan suka ga duk abunda suka mallaka ya zama yayin banza wasu sun yiwa kansu kyamar laili. Ya kamata agaggauta chanja kalar Naira kafin a shiga kanfen Kuma hakan zai tona asirin wasu da ya wa. Ina ji Dansudu




























