An Sace Sarki da Ɗan Kasuwa da Mutane 13 a Alkaleri, In ji Galan Gwana
Daga Maryam Mohammed da Muazu Hardawa, Bauchi
Read also: Iftula’i: Bafadan Sarki ya rasa ransa a ƙoƙarin hana hawa doki a Jigawa
Duk da irin kokarin da Jamian tsaro ke yi wajen ganin an ceto mutanen da yan bindiga suka sace a yankin Alkaleri da ke cikin jihar Bauchi har yanzu tana sama tana dabo, saboda an sace wani Sarki da mutane sha uku (13) da yan bindigar suka yi har yanzu babu labarin su.
Malam Yusuf Gafakar Malaman ƙasar Gwana shine ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci ofishin mu a Bauchi ranar talata a jihar Talata 14/4/2026.
Da farko ya yaba game da kokarin Jamian tsaro na ceto sama da mutane 40 a samamen baya baya da suka kai maboyar yan bindigar cikin makon da ya gabata, ruhoton da suka samu na dauki ba dadi da bata garin na nuna, an kashe da dama daga Yan bindigar kuma an kora su zuwa dajin Madam da wasu dazukan kan iyakar Bauchi da Taraba da Filato.
Yace sun yaba kuma suna ci gaba da adduah kan wannan kokarin da gwamnati ke yi na ganin an samu zaman lafiya a yankin amma har yanzu wasu garuruwan babu kowa.
Malam Yusuf Gafakar Gwana ya kara da cewa a yankin Gwana akwai Sarki wato Jauron Ruga Maikasuwa Malam Bello da aka kama an kai kudin fansa Naira Milyan Uku amma har yau an ki sake shi, sai ko sun saki wasu mutane da suka kama su tara amma har yau babu bayani daga gare su game da matsayin sa.
Ga wasu Labaran:
Sama da ‘Yan Bindiga 150 Sun Nutse a Kogin Sokoto
An Gargadi Ƴan Jaridar Yanar Gizo Da Suyi Aiki da Kwarewa Tare da Ƙare Martabar Kasa
Read also: Masu Zanga-zanga sun ƙone Fadar Sarki da ofishin hukumar NDLEA ƙurmus a jihar Kwara
AN YI KARE JINI BIRI JINI DA YAN BINDIGAR DA SUKA TARWATSA WASU YANKUNAN ALKALERI A BAUCHI
Ya kara da cewa a garin Bunga akwai mutane da aka kama lamarin da ya sa dukkan mutanen garin suka yi hijra zuwa Kashare a jihar Gombe yanzu garin babu kowa sai Jamian tsaro.
Bayan haka akwai Alhaji Isa da matarsa da matar dansa da kuma kanin Bello Mai inji duk an kama su a yankin Mansur suma kowa ya bar garin sai Jamian tsaro kuma babu labarin su.
Ya kara da cewa haka zalika a garin Bagobiri suma kowa ya gudu don tsira da rayuwarsa, haka a garin Digare an kama mutane 10 sun nemi kudin fansa an kai milyan goma sun saki mutane tara sauran na goma Alhaji Bello Maigari yana hannun su bai dawo ba har yau babu lamarin sa.
Saboda haka ne yace dauki daya dayan da ake wa mutane a yankin Gwana da Mansur da Digare da Yalo yana tayar musu hankali kuma har gobe ana zaman dar-dar.
Gwamna Bala Mohammed ya bayyana kokarin gwamnati na shawo kan wannan masala. A saboda haka ne ya nada sabbin sarakuna don kusanto mutane da gwamnati kuma ya gargade su kowa ya bayar da gudummowa don kawo karahen wannan matsala a jihar Bauchi.
Gwamna Bala ya bayyana haka ne a wajen raba sabbin motoci ga sarakunan gargajiya don basu karfin guiwar gudanar da jagorancin mutanen su ta yadda za a samu ingancin zaman lafiya da tsaro.
Read also: Rahoton Kwararu Ya Ce Hare-Haren Garkuwa Da Mutane Ya Ƙaru da Kaso 66% Akan Shekarar 2025 A Najeriya
Har wa yau rundunar Yan sandan jihar Bauchi ta fitar da sanarwar Yan bindiga sun yi kwanton bauna wa Jamian tsaro a wani yankin gandun dajin Yankari yadda suka kashe Jamiin sintiri na vigilante mai suna hambali Alhaji Saadu suka kuma raunata wasu daga cikin su, yayin da jamian tsaron suka bayyana cewa suma sun kashe wani adadi na yan bindigar kuma sun fatattake su daga yankin bayan yin kare jini biri jini a tsakani.
SP Nafiu Habib kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi shine ya bayyana haka cikin wata sanarwar ranar litinin da ta wuce Mai dauke da sa hannun sa.
Ya bayyana cewa Yan bindigar sun farmaki Jamian tsaron ranar lahadi 12/4/2026 da Rana a yankin Mai Ari da ke gundumar Maimadi yadda aka yi kare jini biri jini kafin Jamian tsaron suka shawo kan matsalar suka dawo da zaman lafiya a yankin. Ya zuwa wannan lokacin an tarwatsa gungun Yan bindigar a maboyar su har an kubutar da wasu mutane masu yawa da suka sace.



























