Connect with us

Hi, what are you looking for?

Labarai

Iftula’i: Bafadan Sarki ya rasa ransa a ƙoƙarin hana hawa doki a Jigawa

Sukuwar Dawaki tai ajalin bafade
Sukuwar Dawaki tai ajalin bafade

Iftula’i: Bafadan Sarki ya rasa ransa a ƙoƙarin hana hawa doki a Jigawa

Daga Sunusi K/Na’isa

Tsautsayi ya rutsa da wani Bafaden Sarki a Ƙoƙarin ya hana hawan doki. Lamarin ya faru a garin Gumel ta jihar Jigawa, bayan wani gangamin na sukuwar dawaki da wasu matasa suka shirya ba bisa ka’ida ba.

Bafadan wanda shi yake gadin fadar ta Gumel, mai suna Gada Abdulhadi Mana, ya rasa ransa bayan dawakai sun buge shi a yayin da ya je domin tarwatsa mahayen wanda wasu matsa suka shirya, batare da neman sahalewar mahukunta ba.

A Iya Karanta Wanna:DA ƊUMI-ƊUMI: Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano

Rahotanni sun ce wasu matasa ne a garin na Gumel, ciki har da Ibrahim Gwani da Goni ake zargi da shirya gangamin hawan dawakin ba tare da izini ba, wanda ya janyo tashin hankali a yankin masarautar.

A Iya Karanta Wanna:DA DUMI DUMI:Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré, ya Sake Tsallake Harin Yan ta’adda

Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar Bafadan bayan samun tabbacin mutuwar mai gadin daga likitan asibiti. ‘yan sandan sun ce suna ci gaba da bincike tare da neman waɗanda ke da ruwa da tsaki a tayar da fitinar.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisement

Trending

You May Also Like

Lafiya

Daga Dr. Sunusi U. Na’ibi Yadda mutum ke wanke baki da kuma irin burushin da yake amfani da shi suna iya canza lafiyar baki...

Noma da Kiwo

DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA (2) Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3)...

Noma da Kiwo

Dabarun kiwan kaji a lokacin yanayi na sanyi Daga Yazid Sunusi YahayaRead also: DABARUN KIWON KAJI CIKIN YANAYIN SANYI KASHI NA UKU (3) Sau...

Kano

Gwamnatin Kano Ta ƘirƘiri Sabon Tsarin Biyan Fansho da Giratuti Ta Intanet Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da wani sabon tsari na musamman na...