Shugaban Burkina Faso Ibrahim Traoré, ya Sake Tsallake Harin Yan ta’adda
Shugaban kasar Burkina Faso Ibrahim Traore ya tsira da rayuwarsa a lokacin da wasu gungun Yan ta’adda suka kai masa hari a kokarin su na na habarar da gwamnatinsa, wanda hakan su ta kasa cimma ruwa.
Read also: Chanza Takardar Naira Zai Kawo Ƙarshen Rike Kuɗi a Hannun Yan ta’adda a Najeriya -Ado Dansudu
Shugaban rikon kwarya na ƙasar Burkina Faso, Ibrahim Traoré, wanda zakakurin soja ne, ya tsira daga wani sabon yunkurin kisan gilla da aka kai masa, cikin dare a hanyarsa ta dawowa daga bude wani aiki, kamar yadda majiyoyi daga gwamnati da wasu kafafen yada labarai na cikin gida suka tabbatar.
Makamancin Labarin:Dokar hana bayyana tsiraici: Ibrahim Traore ya sanya biyan tarar Miliyan 2 da ɗauri na dindindin ga wacce aka kama
Read also: Sojoji Sun Dakile Harin Lakurawa, Sun Kwato Makamai da Ceto Dabbobi 62
Rahotanni sun nuna cewa an kai harin ne yayin da shugaban ke tafiya domin duba aiki, inda wasu da ba a san ko su waye ba suka yi kokarin hallaka shi. Duk da hakan, jami’an tsaron shugaban sun yi nasarar kare shi, kuma an samu da dama daga cikin masu yunkurin kisan an hallaka su a fafatawar da akai da su.
Idan za a tuna wannan ba shi ne karon farko da aka yi yunƙurin kashe Traoré ba, wanda ya karɓi mulki a watan Satumba 2022 ta hanyar juyin mulki.
Tun a bayan karɓar mulkin sa, ya fuskanci barazana da dama daga kungiyoyi masu dauke da makamai da kuma wasu daga cikin sojojin da ke adawa da salon mulkinsa.
Read also: Ingila Za Ta Haramta wa Dalibai Amfani da Wayoyin Hannu a Makarantu
Makamancin Labarin:YAN BANGA DA MUTANE 19 SUN RASU A YAYIN ARANGAMA DA YAN BINDIGA A YANKIN DA GWAMNAN BAUCHI YA FITO
A yanzu haka, an kara tsaurara matakan tsaro a kusa da shugaban, tare da aiwatar da bincike domin gano wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin.
Rana24




























