Dokar hana bayyana tsiraici: Ibrahim Traore ya sanya biyan tarar Miliyan 2 da ɗauri na dindindin ga wacce aka kama
Daga Sani Umar
Read also: Rashin Kulawa Na Daga Cikin Bukatun Da Matar Gwamna Abba Ta Kai Kara A Kotu Don A Raba Su
Shugaban Kasar Burkina Faso Ibrahim Traore ya saka dokar biyan tarar miliyan biyu da zaman gidan yari na dindindin ga duk macen da aka kama tana bayyana tsiraicinta a kafafen sadarwa ta zamani.
Ya ce yin hakan babbar illaci ga alu’mma domin yana Janyo sanya shagala ga sabon Allah yana kuma rage kuzarin kishin addini da haddasa bala’i ga ƙasa.
Ka Iya Karanta Wanna:Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta nuna Fina-finai masu dogon zango 22
Read also: Murtala Garo Zai Bayyana A Majalisar Dokokin Kano Don Tantancewa
Shugaba Ibrahim Traore ya bada umarni a rufe dukkanin shafukan yaɗa baɗala na yanar gizo a dukkan faɗin kasar ta Burkina Faso, tare da dakatar da duk wani shirye-shiryan fina-finai dake nuna baɗala.
Ya Ce an san Afrika da kunya gami da martaba al’adunmu da addinimu, amma rana tsaka duk mata sun wasar, wai da suna wayewa.
” A saboda haka ni ba zan lamunci yaɗa fasikanci ba. Ina goyon bayan kaucewa aƙidar turawa”. Inji Ibrahim Traore.
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
A Iya Karanta Wanna:Majalisa Ta Gamsu Da Nasarar Da Wike Ya Samu A Dan Ƙaramin Lokaci A Abuja
Shugaban wanda ke da farin jini na jama’ar da yayi barazanar sanya wando ƙafa ɗaya ga duk mai yaɗa mummunar ta’ada, don haka ya gargaɗi dukkanin masu sana’ar film da su shiga taitayinsu, su kuma suturta jikinsu bisa tsarin koyarwar addini da kuma al’adun ƙasar a lokacin da suke gudanar da sana’ar su.




























