Majalisa Ta Gamsu Da Nasarar Da Wike Ya Samu A Dan Ƙaramin Lokaci A Abuja
Daga Sunusi K/Na’isa
Read also: Ƙaramar Ministar Abuja, Dr. Mariya Bunkure ta Faranta Zukatan Tsofaffin Abokan Aikinta Na AKTH
Majalisar tarayyar Nijeriya ta yaba da gagarumar nasara da bajintar da Mista Nyesom Wike ya nuna a matsayin sa na Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT) a cikin kankanin lokaci.
‘Yan majalisar sun yi wannan yabo ne a lokacin da Wike ya bayyana a gaban su shi da Ƙaramar Minista Mariya Bunkure domin kare ƙudirin kasafin kudin FCT na Naira tiriliyan 1.78 na shekarar 2025.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa na Babban Birnin Tarayya Abuja, Sanata Ibrahim Bomai, ya jinjina wa Wike da Dr Mariya Mahmoud Bunkure, karamar Ministan ta FCT, saboda irin manyan ayyukan da suka aiwatar a karamin lokaci.
Ka Iya Karanta Wanna:Hukumar tace fina-finai ta Kano ta haramta nuna Fina-finai masu dogon zango
Bomai ya ce ya gamsu da tsarin samun kudin shiga da aka tsara na FCT na shekarar 2025, yana mai cewa: “Wannan shi ne karon farko da FCT ke shirin tara har naira tiriliyan 1.78
“Wannan kasafin kudin da FCT ta gabatar yana daga cikin mafiya inganci da aka taba gani.
“Haka kuma, kudin shiga na cikin gida da akayi hasashe zai kai Naira biliyan 608 a 2025 ya nuna babban ci gaba,” in ji shi.
Sanata Abdul Ningi (Bauchi ta Tsakiya, PDP), ya jinjina wa ministan bisa yadda ya sauya fasalin birnin tarayya, Abuja.
Ningi ya kwatanta halin da Abuja ke ciki yanzu da biranen Johannesburg da Cairo, sai dai ya shawarci ministan da ya kara zage dantse wajen inganta tsaro a birnin.
Da yake tsokaci, Sanata Mohammed Ndume (Borno ta Kudu, APC) ya ce: “Duk wanda ya san yadda Abuja take shekaru biyu da suka wuce da yadda take yanzu, ya san cewa ka yi namijin kokari. Inji Ndume.
“Ko jiya abokina ya ce min Wike yana kokari, sai na ce masa a’a, majalisar dattawa ce ke kokari domin ba tare da amincewa da kasafinsa ba, da ba zai iya komai ba”.
Read also: Gwamna Abba Ya Miƙa Sunan Murtala Garo ga Majalisa Domin Sahalewa Ya Zama Mataimakin Sa
Ndume ya tabbatar da goyon bayan majalisar dattawa ga Wike domin ya samu nasara.
A nasa bangaren, Sanata Osita Ozunaso (Imo ta Yamma, APC) ya ce an yi kyakkyawan aiki da kasafin kudin FCT, musamman yadda aka rage kuɗaɗen da za’a kashewa ma’aikata domin kara maida su a manyan ayyuka.
“Sau da dama idan ana tattauna kasafi, mutane kan zo su ƙara kudin da za’a kashewa ma’ikata amma kai ka rage shi da Naira biliyan 21 a kasafin 2025 idan aka kwatanta da na 2024.
“Abu na biyu, kudin manyan ayyuka sun fi na yau da kullum yawa. Wannan abin yabo ne,” in ji Ozunaso.
Sanata Adams Oshiomhole (Edo ta Arewa, APC) ya bayyana Wike a matsayin ɗaya daga cikin ministocin da suka fi kowa kokari a gwamnatin APC.
Oshiomhole ya ce a baya ana kashe kuɗaɗe masu yawa kan abubuwan da ba su da amfani yayin da ake barin ayyukan more rayuwa, amma Wike ya kawo sauyi mai ma’ana.
Ya kuma yaba wa Wike da shirye-shiryen da ya aiwatar domin inganta rayuwar jama’a a karkara.
Ya ce wannan babban mataki ne na rage cunkoso a cikin birni ta hanyar kai ci gaba inda mutane ke zaune.
Sanata Ireti Kingibe (FCT, LP), wadda a baya ke daga cikin masu suka ga salon shugabancin Wike, itama ta bayyana cewa ayyukan da ministan ke yi yanzu babu abin kushewa.
A majalisar wakilai, Shugaban kwamitin FCT, Mista Muktar Betara, ya cira wa Wike tagiya kan sauyin da yake kawowa a Babban Birnin Tarayya, tare da fatan dorewar hakan.
Sauran ‘yan majalisa suma sun nuna jin dadinsu kan yadda ministan ke ƙoƙari wajen kawo ci gaba da amfanar jama’a a ƙarƙashin manufar “Sabon Fata” na Shugaba Bola Tinubu.
Ka Iya Karanta Wanna:Majalisar Matasan Arewa ta nuna damuwa da matsanancin rashin wutar lantarki a Kano
Read also: “Babu Wani Dalilin da Zai Sa Na Yi APC”, Wanna Wasan Fulani Ne da Kanuri – Sule Lamido
A ƙarshe, Wike ya roƙi ‘yan majalisar da su amince da ƙudirin kasafin kudin na FCT na Naira tiriliyan 1.78 na shekarar 2025.
Ya bayyana cewa daga cikin tiriliyan 1.78, an ware Naira tiriliyan 1.28 domin manyan ayyuka, wanda ya kai kashi 72.3 cikin 100, yayin da Naira biliyan 494.1 za su je kan kudin yau da kullum, wanda ya kai kashi 27.7 cikin 100.
(Dokin Ƙarfi Tv)



























