Wasu Fusatattun matasa sun kashe DPO ‘Yan Sanda har lahira a Kano
Wasu Fusatattun matasa a Karamar hukumar Rano sun fara wa Baturen ‘yan Sanda na yankin har ofishinsa, wanda hakan yai sanadin rasuwarsa.
Read also: An Kama Umar Da Wasu Matasa 2 Da Ake Zargi da Kashe Matar Aure Da ‘Ya’yenta 6 A Kano
Majiyarmu ta ce matasan sun aikata wannan danyan aiki ne bayan da suka sami bayanin DPO ya yiwa abokin su duka wanda har ya ta kai ga sanadin rasuwarsa.
Samun labarin ke da wuya matasan sukai gungu inda suka iske jami’en tsaron har ofis, kuma ana mai faruwa ta faru.
A Iya Karanta Wanna:Dokar hana bayyana tsiraici: Ibrahim Traore ya sanya biyan tarar Miliyan 2 da ɗauri na dindindin ga wacce aka kama
Majiyar ta ce fusatattun matasa sun farwa Ofishin ‘yan sandan bisa zargin ya kashe wani ɗan uwansu, da ake zargin ya karya doka ta gudanar da wani gangamin rally a babura.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da rasuwar DPO na Ƙaramar hukumar Rano a wata sanarwar da Kakakin rundunar ‘yan sandan, Abdullahi Haruna Kiyawa ya a daren Litinin.
Ya ce tuni an kama mutane 27 da ake zargi da hannu a cikin lamarin, tare da tabbatar da dawo da zaman lafiya a yankin na Rano.
Read also: ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 3, Gami Da Garkuwa Da Wasu A Kano
A Iya Karanta Wanna:‘Yan sanda a Kano Sun Chafke Likitan Bogi da Wani Matashi Bisa Zargin Zubar da Ciki Da Aikata Kisan Kai
Abdullahi Kiyawa ya ce Kwamishina ‘Yan Sanda na Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori ya bada tabbacin rundunar zata gudanar da bincike tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kuliya.




























