Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshan jihar Kano ta ce ta kama wani matashi Ukasha Muhammad bisa zargin yi wa ‘yar uwarsa Amina Bala, mai Shekara 19 ciki da kuma Likitan bogi da haɗin baki wajen kashe ta, bayan yayi mata allura da Kuma magunguna da ya bata da nufin zubar da ckin a ƙaramar hukumar Tofa.
Kakakin rundunar ‘Yan sanda na jihar Kano, SP Abdullahi Kiyawa ya sanar da haka ga manema labarai.
Read also: Hukumar Shari’a da Rundunar Yan sanda a Kano za su kawo karshen faɗan daba da kwacen waya
Sanarwar ta ce runundar ta cafke Ukasha Muhammed ne bayan ta samu rahoton cewa ya yi wa Amina Bala mai shekara 19 ciki, sannan ya kai ta wajen wani mai suna Chidera Ugwu don ya yi mata allurar zubar da cikin.
Read also: Jami’in KAROTA Yayi Sanadin Kama Wani Da Ake Zargin Barawan Mota da Kuma Kungiyar Su A Kano
Sanarwar ta kara da fadin Ugwu, wanda likitan bogi ne, ya yi mata allura tare da ba ta wasu ƙwayoyin magani da zimmar zubar da cikin, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwar ta.
“An kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifukan da ake zargin sun aikata,”
Read also: Matashi Mai Shekara 24 Ya Kashe Mahaifinsa A Bauchi
Bincike ya nunar da cewa da ma Ugwu ya dale yana aikata wannan mumunar halin na yi wa mata masu ciki allurar zubar da cikin wanda hakan ke sanadiyar rasa rayukansu”.inji kiyawa.
Rundunar ta ce zata kammala bincike ta kuma gurfanar da su gaban kotu domin su karbi sakamakon abin da suka aikata nan bada dalewa ba ko ya zama izina ga masu aikata laifi.




























